Labaran Yau

Gwamnatin Tinubu Ta Saka Hannu Kan Karin Albashin Tinubu, Shettima Da..

Gwamnatin Tinubu Ta Saka Hannu Kan Karin Albashin Tinubu, Shettima Da..

A yau ne fadar shugaban kasar Nigeria Bola Tinubu ta saka hannu a kan takardar karin albashin shugaban kasa, mataimakin sa da kuma sauran manyan mukaman fadar ta shugaban Nigeria din.
Jaridar Daily trust ce ta wallafa wanna labari, inda ta bayyana cewa ofishin Tara kudade da kuma bin kadin su wato RMAFC ta tabbatar da karin albashin da kashi 114% ga dukkanin zababbun `yan siyasar na tarayya.

Ba da dadewa ba hukumar ta gama tsare tsare da shirin aiwatar da wannan chanji ga yan siyasar na kasar.

Tinubu And Kashim
Tinubu And Kashim

Duk da cewa hukumar ta bada shawarar karin albashin kafin gwamnatin Tinubu ta karbi mulki amma gwamnatin tarayyar bata saka hannu a kan takardar karin albashin ba sai yau.

Labari na karya ya zagaya a yanar gizo `yan kwanakin da suka shige inda ake cewa karin ya hadar da shugaban kasa, mataimakin sa da zabbabun maikatan gwamnatin tarayya da na jiha da maaikatan kotuna.

Jaridar Daily trust ta bada labarin cewa hukumar da taimakon fadar gwamnatin tarayyar ta tabbatar da karin albashin da kashi 114% ga dukkanin zababbun maaikatan gwamnatin tarayya a kasar ta Afrika maso yamma.

Yan Kasuwan Man Fetur Sun Karyata Karin Kudin Mai Zuwa 700

Yan Kasuwan Man Fetur (IPMAN) Sun Karyata Karin farashin Kudin Mai Zuwa naira 700 a kan kowani lita a fadin kasar.

Ciyaman na IPMAN na kudu maso Yamma, Dele Tajudeen, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da akayi dashi ranan jumma’a a Ibadan tare da Hukumar labarai ta kasa.
Ga cikakken labarin akan Man Fetur A Yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button