Labaran Yau

Abinda Yasa Na Sayar Da Filin Da Aka Mai Shaidar Rusawa – Shugaban Hukumar Rashawa Ta Kano

Abinda Yasa Na Sayar Da Filin Da Aka Mai Shaidar Rusawa – Shugaban Hukumar Rashawa ta kano

Muhuyi Magaji Rimingado, ciyaman na kwamishan din korafi da yaki da rasawa ta kano ya bayyana siyar da filin da yayi wanda aka zana shaidar rusawa.

Daily Trust ta rawaito cewa gwamnatin gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi maki wa gine ginen da zata Rusa.

Aciki akwai akwai shaguna da gidajen Mai, wanda ke hanyar BUK road. Da gine ginen da akayi cikin kwaryar garin kano ta tsohuwar garun kano badala.

Ismail Bello daya daga cikin masu gine ginen a BUK Road. Ya bayyana cewa ya samu filin a hannun shugaban Hukumar Rashawa ta jiha.

Dan kasuwan ya zargi gwamnatin da yin abinda bai dace ba na rushe rushe bayan wasu filayen an siyosu ne ta hanyar doka ta hannun wanda suke da connection da wannan gwamnati.

Rimingado, shi ne wanda dan kasuwa ya bayyana wanda ya siya fili a hannun sa. Ya fadawa daily trust cewa ya siya ne da tabbacin cewa filin ba ta ha’inci bane dan ya gamsu da binciken sa.

Yace ginin ba ya cikin Makaranta ko masallaci Kuma bai ma shafi tsohuwar Bangon garin Kano ba.

Kuma ya siya filin a naira miliyan sha biyar.

Yace a yadda ya sani, Kuma gwamna zai iya bada fili wa koma waye. Ya kara jaddada hakan.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button