Labaran Yau

Hukumar NIMET Ta Bayyana Cewa Za Ayi Hazo Na Kwana Uku

Hukumar NIMET Ta bayyana cewa za ayi Hazo na kwana Uku

Hukumar Nimet ta Najeriya, ta ambaci cewa za ayi hazo da walkiya cikin kwana Uku, daga Litinin zuwa laraba a fadin kasar.

NIMET ta sake yanayin weather ranan lahadi a Abuja yayin da ake jiran sakamakon bincike ta hazo ranan ranan Litinin. Da Kuma tazara ta rana a yankin Arewa da kuma walkiiya na safiya a wajajen taraba da kebbi.

A bayanin Hukumar, Akwai Alamun walkiya a yankin Borno, Adamawa, Bauchi, Gombe, Kaduna, Taraba, Kano, katsina, Zamfara da kuma kebbi wanda zai iya yiwuwa da rana.

“Hasashe ta bayyana da yiwuwar hazo a yankin arewa ta tsakiya da kuma ruwan sama da Safiya a yankin birnin tarayya, Kogi, Nasarawa da kuma Benue.”

NIMET ta yi hasashen walkiya da ruwan sama a mafi yawan yankuna da rana.

“Yanayi na hazo zai bayyana garurukan kudu da alamu na ruwan saman safe a yankin ebonyi, Akwa Ibom da cross river.

“Ruwa sama zai iya fadi a wannan wajejajen jifa jifa da rana ko yammaci” a cewar.

A bayanin NIMET, rana zai bayyana da Kuma hazo kadan a yankin Arewa da safe ranan talata.

Walkiya a yankin Adamawa, Taraba, da jihar kaduna da rana.

Ranan laraba, NIMET ta bayyana cewa za ayi rana da hazo a yankin arewa maso gabas ta yankin Borno, Yobe, Taraba da Adamawa.

A wuraren da ake jiran yiwuwar walkiya da tsawa, iska mai karfi zai iya fin ruwan sama, bishiya, pole wire da gine gine wanda basu da karfi zasu iya fadi.

Hukumar NIMET Ta Bayyana Cewa Za Ayi Hazo Na Kwana Uku
Hukumar NIMET Ta Bayyana Cewa Za Ayi Hazo Na Kwana Uku

“Ana Jan kunne wa mutane da su Zauna a waje daya ko cikin gida dan gujewa tsawa.

“Duka jiragen sama da masu gudanar da jiragen ake bawa shawaran su na bincikan rahoto na yanayi lokaci lokaci a NIMET dan gudanar da aiki Mai tsari da inganci.

“Ana shawartan mutane dasu kiyaye da Kuma daukan matakai da suka fi da wajen kula da lafiya da dukiyan su a wannan yanayi na Damina” a cewar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button