Labaran Yau

Mutum 27 Na Tsare Hannun Yan Sanda Kan Laifukan Fashi, Kisa, Tsafe Tsafe Da..

Mutum 27 Na Tsare Hannun Yan Sanda Kan Laifukan Fashi, Kisa Tsafe Tsafe Da Sauran Su

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta ce jami’anta sun kama mutane 27 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, ayyukan kungiyar asiri, da kuma kisan kai.

Kwamishinan ‘yan sandan Legas, Idowu Owohunwa wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a Legas, ya ce an kwato muggan makamai da alburusai daga hannun wadanda ake zargin.

Ya ce, “Muna da mutane 27 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban da suka hada da fashi da makami, kisan kai, kungiyar asiri, barna, da dai sauransu.

“Daga dukkan wadannan shari’o’in da muka samu nasarar fatattakar su, mun kwato jimillar makamai guda shida, alburusai 12, wuka daya, babura biyu, mota daya, da katin SIM”.

Owohunwa da yake ba da bayani kan laifuka daban-daban da wadanda ake zargin suka aikata, ya bayyana cewa an kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne, Kesari Confraternity, wadanda suka shirya daukar fansa kan mutuwar shugabansu a yankin Mushin da ke jihar, a ranar 30 ga watan Yuni.

“Jami’an ‘yan sanda sun kai farmaki inda suka kama mutane hudu: Tobi Robert, mai shekaru 23; Opeyemi Adeosun, 22; Jenkeo Olumide, mai shekaru 20; Toheeb Tajudeen, 25; da Nurudeen Kazeem, 27.

Ya kara da cewa bincike ya nuna cewa su ’yan fashi da makami ne, gungun kungiyoyin asiri da ke ta’addancin Mushin da kewaye.

Shugaban ‘yan sandan na Legas ya yi nuni da cewa wadanda ake zargin sun amsa cewa su mambobi ne na kungiyar Eiye Confraternity, yana mai tabbatar da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin kamo sauran ‘yan kungiyar da suka gudu tare da kwato wasu makamansu na aiki.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Legas, Ben Hundeyin, Sufeto na ‘yan sandan ya kara da cewa an kuma kama wasu ‘yan kungiyar Eiye confraternity guda biyu a yankin Ebute-Metta a ranar Talata a yayin da suke yin amfani da makamai domin su je su kai farmaki kan ‘yan kungiyar asiri a yankin guda.

Ya ce ‘yan sandan sun kama wasu mutum 10 ciki har da wata mace a Iba Okokomaiko bayan sun kashe mutum daya mai suna Ojo Lion.

“Wadanda ake zargin sun amsa cewa su mambobi ne na kungiyar Eiye confraternity. An kwato bindigogin ganga guda da aka kera a cikin gida tare da harsashi masu rai guda biyu a hannunsu,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button