Rundunar ‘yan sanda ta musamman a kan harkokin man fetur da haramtacciyar hanya, da ke aiki a karkashin babban sufeton ‘yan sandan kasar ta kama wata kungiyar masu laifi da ke da hannu wajen safarar da tace man fetur zuwa kasar Kamaru.
A watan Yuli, rundunar ta kwato manyan motoci 13 cike da danyen mai, dizal, da man fetur da aka sace. Sun kuma kama mutane 17 da ke da alaka da wadannan laifuka.
Olumuyiwa Adejobi, kakakin rundunar ‘yan sandan Najeriya ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Abuja, tare da Bayo Sulaiman, Kwamandan Task Force. An kama mutanen ne a jihar Adamawa.
A ranar 13 ga Yuli, 2024, rundunar ta kama wasu motoci kirar Toyota Corolla guda uku a Adamawa. Motocin dai na dauke ne da jarkokin mai guda 130, motar daya dauke da gwangwani 50, sauran biyun kuma dauke da gwangwani 40 kowanne.
An kama wadannan motoci da kayansu, an kuma tsare wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda ta Girei.
Sulaiman wanda ya nuna wa ‘yan jarida motocin da aka kama, ya ce an gurfanar da dukkanin wadanda ake tuhuma 17 a gaban kotu.
Ya kuma jaddada cewa wadanda ake zargin suna gidan yari ne ko kuma suna fuskantar shari’a, kuma motocin da sauran kayayyakin da aka kama yanzu mallakar gwamnati ne.
Rundunar ‘yan sandan dai na kokarin ganin ta samu amincewar kotu domin bata wa gwamnati kayayyakin da aka kama har abada, kuma ta mayar da hankali wajen samun hukunci a kan wadannan shari’o’in.