Labaran Yau

Yajin Aiki: Hukumar Filin Jirgin Sama Ta Kasa Ta Ce Wa Fasinjoji Da Su Nemi Mafita

Yajin Aiki: Hukumar Filin Jirgin Sama ta kasa ta ce wa Fasinjoji da su nemi mafita

Ma’aikatan Hukumar filin jirgi na babban filin jirgin Na Nnamdi Azikiwe, sun bayyana cewa fasinjoji su nemi wata hanyar yin tafiya dan kar su tozarta.

Jami’an sun bayyana ran litinin a Abuja, cewa duk wasu qalubale da za a fuskanta ba da niyyan cin mutunci bane Kuma Suna da nasani.

Sun bayyana cewa zasu tafi yajin aiki na kwana biyu dan gargadi wa gwamnati, wanda zasu fara yau litinin.

DOWNLOAD MP3

Jami’an Suna bayyana wa jama’a akan cewa filin jirgin yana bude dan gudanar da wasu lamuran filin jirgi amma kuma jirage barasu tashi ba.

Ita union din ma’aikatan filin jirgin sun bayyana cewa zasu katse aikin tashin jirage a Najeriya ranan Litinin da talata.

Yajin aikin yasamu haddin kai da goyon bayan
Jiga jigen ma’aikatan filin jirgi na kasa… Kuma sunce ba janyewa har sai sun cika kudirin su na yajin aikin, saboda a biya musu bukatunsu na biyan su mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta saka wanda har yanzu bai shiga Albashin nasu ba.

DOWNLOAD ZIP

Da Kuma biyansu sauran kudaden su da suke bi tun 2019, wanda ya hada da na NIMET, NAMA, Nigeria Civil Aviation Authority, Da NCAT Zaria.

Sakatare janar na yan union din sufuri na kasa ocheme Aba yace su barasu saurari tattaunawa daga bakin wani ba Sai dai aiwatarda abinda suke Nema.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button