Labaran YauNEWSPolitics

“Ba maganan Sheik Bane Ya Tinzira” – Muhammad Zakariya Zuwaga Comrade Pantami.

Zaben Shugaban Kasa 2023: Ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka.

Zaben Shugaban Kasa 2023: Ruwa cikin cokali ya isa mai hankali wanka.

Kamar yadda Comrade Pantami yace a shafin sa ta yanar gizo.

“Wallahi fitowa fili kiri-kiri da Sheikh Jingiri yayi yace a yi Muslum-Muslum Ticket shine dalilin fusata kiristocin Najeriya akan zaban Peter. Domin kafun ya fadi hakan akwai Fastoci da yawa a Coci da suka dinga cewa kiristoci kada su zabi Peter bazai kai labari ba, amma daga karshe aka fusata su. Magana ta gaskiya zaben kabilanci bazai kawo mana cigaba ba, balle har a samu hadin kai.”

DOWNLOAD MP3

Muhammad zakariyya “Sheikh Thani yahya Jingir ba sa’an ka bane ka kiyaye furucin ka akan shi,

In bada rashin tunanin da sanin ya kamata wai kace maganar Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ne ta tunzura kristoci suka zabi Krista.
Idan baka bincike kuma baka da tarihin bari kaji yadda lamarin take kafin maganar Sheik Afenifere da ma manyan kristoci yan siyasan Arewa irin su Yakubu Dogara da Babacir lawal da makamantansu da dama suka bayyana kiyayyarsu a fili akan zabin da akayi na musulmi da musulmi.”

“Abin da mamaki sosai har dan Majilisar na APC Kirista yace shi baya goyon bayan Muslim Muslim tickets kuma bazai zabe su ba baka iya masa raddi ba sai malamin addini wanda ka raina ko!

DOWNLOAD ZIP

Ka sani cewa Dogara, duk da kasancewarsa dan APC, amma bai hanashi barranta da APC ba saboda kin kiyayyarsu wa Musulunci, amma Malam Sani Yahya Jingir shi ne ka tsana sabo daya bayyana kaunarsa da Musulunci?

Ko ka manta ne da maganar da Dr,kayode Fayeni Gwamnar Jihar Ekiti wanda yake cewa kungiyar CAN na jihar sa a wata bakwai na 2022 cewa basa goyon bayan zabin Muslim- Muslim,ama tsarine na neman shugabancin duk da cewa akwai kiristoci masu dukan kamalar da za’a zaba a Arewa amma tambaya shin an samu?
Taya za ayi ace inda Muslimi suka fi yawa ace wani wanda ba Muslimi ba zai wakilce su bayyan muna da wadanda suka cencenta.”

“Dogara a taron kiristoci na Arewa da pastoci da suka yi aduaoin da bada shedar yabo a garin Jos ya bayyana cewa ya zama dole dukkan kiristoci na Nijeriya su kauracewa zabin Tinibu, shin idan shi Tinibu ya dauke Muslim shi gogan naka Atiku ba Kirista ya dauka ba!?
Mai yasa basu ce a goyi bayan shiba!

Sanata Oji Uzo kalu yace shi bai ga wani abin tada hankali ba domin kuwa kowace Jam’iyyar siyasa tana so tayi nasara ne a zaɓen ta yace ba yada za ayi ace Tinibu ya dauki Kirista wanda basu da yawa a Arwa ace shine zai wakilce Arewa.

A watan goma ne 2022 gama yan mabiya APC karkashin Jagorancin Yakubu Dogara da sauran shuwagabannin kamar su Babachir Lawal, suka ce basa goyon bayan Zabin APC kuma zamu san yarda zamuyi domin mu hana su samun nasara.”

“Muna so ka fimata cewa sunyi wannan ne domin kiyayyarsu ga Muslunci.

Daga karshe ina so kasani cewa Kiristoci da dama sunyi video tun kafin sheik yayi magana sun bayyana ra’ayin su na cewa duk wani mabiyan shi ya zabi Peter Obi.
Idan baka sani ba har majamiar su basa bari mabiya ya shiga sai ya nuna katin Zabe.
Muna kiran ka da babban murya karka kus kura ka sake ambaton sunan Jagoran mu a lamurran ka na siyasa domin neman suna ko daukaka a idon mabiya.
Sheikh ba irrin mu bane yan baranda media masu neman like ko Mabiya.
Muna baka shawara ka janye kalamun ka matukar kana son kimar ka da darajar ka ta dawo a idon masoyansa domin mu bamu da shugaban irrin sa, muna girmama shi domin yan daura mu akan hanyar addini !!

Sakodaga

Muhammad Zakariya Musa zuwa ga Comr Abba Sani Pantami.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button