Karamar Yarinyar Data Lashe Gasar Qur’an Ta Duniya A Dubai
Karamar Yarinyar Data Lashe Gasar Qur’an Ta Duniya A Dubai.
Sunanta Hafiza Aindati Sisi daga Kasar Senegal, itace wacce tazo na daya a gasar Karatun Al-Qur’ani na duniya izu sittin na mata da ya gudana a Kasar Dubai
Abinda ya burgeni, bayan ta dawo Kasarta, sai mutanen Kasar suka shirya rali suka mata kyakkyawan karba saboda kwazon da ta nuna a fagen haddar Al-Qur’ani Maigirma
Sai na fahimci lallai Al-Qur’ani Maigirma yana da kima sosai a Kasar Senegal, kuma suna kaunar ma’abota Al-Qur’ani Maigirma tare da girmamasu
Yaa Allah Ka kara mana riko da LittafinKa Al-Qur’ani Maigirma, Kasa ya cecemu ranar Hisabi