Illolin Bayyana Zunubi Na Dr Sani Umar Rijiyar Lemo
Allah mai gafara ne kuma mai jin kai, Allah ka hanamu aika abu sai muka aikata shi, Ubangiji ka gafarta mana, ka mana sitira akan wannan ka rufa mana asiri kada wani ma daga cikin halittun ka yasan Mun aikata wannan laifin, daga mu sai kai, ka rufa mana asiri a lahira.
Malam yace wannan shine gafara, gafara shine Allah ya rufa mana asiri, kayi laifi ubangiji ya suturta ka, shiyasa Allah SWT yake yafewa kowa Banda wanda suke fitowa suna gama gadi suna yi wa Allah laifi, suna nuna wa kowa suna laifi kaza.
Zaka ga yanzu a tiktok ko instagram mace ta fito tana nuna tsaraici wa duniya, a da can zakaga dama anayi da wasu tsiraru wanda dama aikin laifin ne ya hadasu. Amma Yanzu Ana nunawa kowa da kowa, da wanda yakeso da wanda bayaso kowa za a nuna masa.
Annabi yace duk Al’umma ta na iya samun afuwa Amma Banda wanda bayi boye laifi. Wanda barasu boye laifinsu ba, zasu fito suna bayyana wa, mutum ya kwana yana laifi ko cikin duhu ya fito da safe Yana fadi, to in Allah ya yi wa ko wa afuwa banda wannan. Bare samu afuwar Allah ba.
Saboda haka Gafarar ubangiji shine Allah ya maka sitira ya lullubeka kai dashi kawai babu Wanda yasan mai yake gudana. To wannan ita ake cewa Gafara.
Adduar Neman Gafarar Ubangiji
“Allahumma anta Rabbi la ilaha illa anta, Khalaqtani wa ana `Abduka, wa ana `ala `ahdika wa wa`dika mastata`tu, A`udhu bika min Sharri ma sana`tu, abu’u Laka bini`matika `alaiya, wa abu’u laka bidhanbi faghfir lee fa innahu la yaghfiru adhdhunuba illa anta.”
An samo a Sahih al-Bukhari 6306
Fadin “astaghfirullah” kamar sau dari da safe da kuma yamma Yana da falala masu dumbun yawa.
“Allahumma anta rabbi la ilaha illa anta, khalaqtani wa-ana ‘abduk, wa-ana ‘ala ‘ahdika wawa‘dika mas-tata‘t, a‘oothu bika min sharri ma sana‘t, aboo-o laka bini‘matika ‘alay, wa-aboo-o bithanbee, faghfir lee fa-innahu la yaghfiru-thunaba illa ant”
“Subhanakal-Lahumma wa bihamdik, ash-hadu allaillaha illa ant, astaghfiruka wa’atoobu ilaiyk”
“Allahumma inni astaghfiruka li dhanbi wa as’aluka rahmatak”
“Allahummaghfirli khatāyaya wa dhunubi kullaha”
“Rabbana la tu’a-khidhna in-nasina aw akta’na, Rabbana wa la tahmil ‘alaiyna isran kama hamaltahu ‘alal-ladheena min qablina. Rabbana wala tuham-milna mala taqata-lana beh. Wa’fu-‘anna, waghfir-lana war hamna, Anta maulana fansurna ‘alal qawmil kaafireen”
“Allahumma inni astaghfiruka li kulli dhambin”
Allah ya yafe mana zunuban mu, ya suturta mu ya kuma kare mu.
Domin samun fatawowi da addu’o’i, biyo Shafin mu ta labaranyau.com, Muna kawo muku abubuwa na ilimi wanda zai kare mu gabadaya.