Addini

Falalar Sallan Dare na Dr Isa Ali Pantami

Falalar Sallan Dare na Dr Isa Ali Pantami

Qiyamul layli sunnah ce muhimmiya, fa’idodinta na kare lafiyar ka da imaninka Allah ne kadai yasan adadinsu. Mafiya yawan wanda suke qiyamul layli tsakaninsa da Allah, toh tsakaninsa da Allah bai cika lalacewa ba, indai mutum zai yanke barci cikin dare ya tashi yayi ibadah toh Allah zai kare sa kuma Allah baya bari tsakaninsa da bawan sa mai sallar dare ya baci.

Allah Yana kare su, Yana tumbuke musu bala’i da musiba. A kullum anaso ka samu minti 30 zuwa awa daya ka ta shi kayi ibada, kuma daren nan akwai lokutan da ake karban addua, kana yin addua kamar bakin wuka ya tafi. A take Allah yake karba Allah baya maida adduan dare. In har ka tashi kayi sallah kayi addua Allah zai amsa maka. In mutum ya saba qiyamul layli, iya daga cikin asara a rayuwa ace wani dare da zai wuce bai yi qiyamul layli ba.

DOWNLOAD MP3

In mutum ya saba zai fahimci hakan, ji yake ya fara azumi ya wuce suhur bai yi suhur ba. Ko kuma lokacin buda baki yayi bai samu abin bude baki ba. Shi yasa idan Allah yasa muka saba da qiyamul layli zaka ga akwai nishadi, akwai halawa, dandano a cikin sa. Kuma zaka ga bakayi asarar daren ka ba, kuma ayi sa’a ka samu asuba ka kuma cin riba, kuma zaka tashi cikin kariyar Allah SWT, sai yasa qiyamul layli muhimmin abu ne. Muyi kokari muga mun dage munyi ibadah dan bauta wa Allah SWT muyi addu’o’i muyi sallah mu tsarkake zuciya mugayawa Allah bukatun mu, Alkawarin Allah ne cewar zai amsa mana.

DOWNLOAD ZIP

Musamman masu hirar dare wanda ke kai karfe 12 zuwa karfe 1 kamin kayi barci to ka dage kayi kamin ka kwanta.  In kuma zaka iya tashi bayan ka kwanta karfe 1 dare toh tashin yafi falala.

Kalli bidiyon a kasa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button