AddiniFeatured

Addu’o’i Da Ake Bukatar Mace Tayi Lokacin Nakuda

A lokacin da Mace mai ciki ta fara nakudan haihuwa, Malamai sun hadu kan fatawar cewa Ana bukatar mace ta yawaita fadin wannan addua domin samun sauki yayin haihuwa.

Adduar tana nan kamar haka: “Ya Hayyu Ya Qayyum bi rahamatika astagith, La’ilaha Illahuwal Azimul Halim, La’ilaha Illahuwa Rabbus samawati wal ard wa rabbul arshil karim. Allahumma Rahmatika arju fal takil ni ila nafsi darfata ayn. Wa aslih lee sha’ani kulla.

Laa ilaha illa anta, Allahumma laa sahala illa ma Ja’altahu sahla anta taj’alul hazna izha shi’ita sahal, Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai’a. La’ilaha illa anta subhanaka inni kuntu Minaz zwalimin”.

Nakuda
Nakuda

Ma’anar da ita wannan addua ta kunsa yana nan haka: “Ya Allah kaine rayayye kaine dawwamamme cikin rahamarka cikin rahamarka nake neman Agaji, Lallai na shaida babu wanda ya cancanta a bauta masa da gaskiya sai Allah shi kadai. Ubangijin Sama Ubangijin Al’arshi mai girma.

Allah ina kaunar rahamarka cikin nakudar da nake ciki, Allah karka barni cikin halin da nake ciki daidai da yadda bawa ke kifta ido, Ya Allah inka saukakamin babu wanda ya isa ya tsananta min, inka tsananta min babu wanda ya isa ya saukaka min. Allah Allah Allah kaine Ubangiji na Kai nake Kira nake neman taimako. Allah bani da wanda zan nemi taimakonsa sai kai, Lallai Allah ka tsarkaka ni baiwarkace na zalunci kai na”.

Sai Kuma Ta fadi Wannan: ”Rabbi yasir wala ta’asir” yana nufin Ya Allah ka saukake min, karka tsananta min” Ana so mai nakuda ta yawaita wannan addua.

Da kuma Ayah a Qur’ani cikin Suratul Abasa “Thummas-sabila yassara”
Yana nufin “Allah ya kawo hanya mai sauki”

Shima Ana bukatar Mai nakuda ta yawaita fadin wannan ayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button