AddiniLabaran Yau

Abinda Musulmi Yakamata Yayi In Ya Shiga Damuwa

Abinda Musulmi Yakamata Yayi In Ya Shiga Damuwa 

Duk wanda wani abu ya dameshi Sai ya tashi yayi alwala, cikakkiyar Alwala ta nutsuwa, sannan mutum ya tashi yayi sallah Raka’a biyu.

Wanda a wani hadisin Annabi SAW yace” Laa yu haddithu fihi ma nafsahu, wanda yayi sallah saboda bai tuna kowa ba Sai Allah. Ya idar da sallar sa. Wannan sallar ana kiranta salatul haajah”.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Annabi SAW yace ”A’adaa’ul lahu maa sa’al, Duk abinda ya roka Allah zai bashi”. Shi yasa mutane dayawa dake cikin wata damuwa, ko kunci tayi yawa a garesu, shawarar da zaka basu shi ne madadin mutum yaje yayi roko, ko ya shiga abinda zai taba mutuncin sa, ko yayi asarar dukiyar sa, shine babu abinda ya gagari Allah.

Allah yana jinka kamar yadda yake jin kowa, Allah zai iya amsa maka kamar yadda yake amsa wa kowa. Tashi cikin dare, musamman a cikin thuluthul laylil Akhi, kayi Alwala kayi nafila raka’a biyu nutsatstsu, kasa goshinka a kasa Kace Ya Allah Ina nema a ban, Ina neman kariya a kare ni, ya Allah Ina neman tsari a tsare ni, Ya Allah Ina neman abu Kaza ka ban.

Manzon Allah SAW yace Duk abinda ka nema Allah zai baka. Albani ya inganta hadisin Ibn Janini cewa Manzon Allah SAW yace Duk abinda yake damunka kaje kayi sallah zaka samu waraka.

Nana Aisha R A tace indai kaga Annabi SAW ya samu matsala to kawai zuwa yake yayi sallah, Sai ya samu maganin matsalar, haka kaima.

Sai wani yazo yace ma Annabi SAW abu Kaza ya dameni, Annabi yace je kayi sallah, yana zuwa yayi sallah yana dawo wa yace wa Annabi SAW bukata ta samu. dan Haka wannan lakani ne daga Manzon Allah SAW akan kowace bukatar ka.

Wasta’inu bissabr wassalah ku nemi taimako a wajen Allah wajen Hakuri da sallah, Sallah Tana da nauyi Sai dai wa ga masu Tsoron Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button