Advertisements
Gwamnatin Tarayya Ta Ki Tayi Murabus Shugabancin NDLEA Da NAFDAC
Gwamnatin Tarayya batayi Murabus wa shugabancin Hukumar kula da Miyagun kwayoyi ta NDLEA da Hukumar kula da magunguna da abinci ta NAFDAC, bayan umarnin murabus wa shugabancin hukumomin gwamnati.
Willie Bassy, daraktan zantarwa na ofishin sakataren gwamnatin tarayya ya bayyana hakan ranan talata a Abuja.
Hukumar labarai ta kasa ta bayyana cewa shugaban kasa ya Amince da Murabus Na shugabancin hukumomi, jami’u da kampanonin gwamnati.
Advertisements
A bayanin Mista Bassy, sakataren gwamnatin tarayya George Akume ya bayyana cewa murabus din bai shafi Hukumar NDLEA da NAFDAC ba.
“Duba da umarnin Murabus na hukumomi da jami’u da kampanonin gwamnati na kasa.
“Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana cewa shugabancin Hukumar kula da miyagun kwayoyi ta NDLEA da Hukumar kula da abinci da magunguna basu cikin wanda aka umurta dan yin Murabus” a cewar sa.
Advertisements