Labaran Yau

Abdulrasheed Bawa Ya Shiga Hanun DSS

Ciyaman din Hukumar yaki da laifukan kudade EFCC ya samu dakatarwa daga kujerar sa. Tsohon shugaban Hukumar EFCC ya kasance a fadar shugaban kasa a safiyar yau inda ya kai wa shugaban kasa Bola Tinubu rahoto kan aikin su.

Bawa ya kasance Wanda ake zargi da hanu dumudumu wajen karbar rashawa, tun kamin Tsohon gwamna Matawalle ya bayyana zargin cewa ya nemi Cin Hanci  na Dala Miliyan 2.

Da Yamma cin Laraba, Shugaban Kasa Tinubu ya bada umarnin dakatar da shugaban EFCC wanda hakan zai bada daman aiwatar da binciken yanda yakamata.

DOWNLOAD MP3

.Abdulrasheed Bawa

A halin yanzu, Abdulrasheed Bawa yana hannun Hukumar tsaro masu Farin kaya DSS. An samu rahoton cewa Bawa ya isa babban Ofishin DSS da karfe 9 na dare.

Wani ya bayyana cewa Yanzu haka yana cikin dakin bincike domin ansa tambayoyi.

DOWNLOAD ZIP

Mai magana da yawun DSS Peter Afunanya ya tabbatar da yana hannunsu wa jaridar daily trust Kuma bai bayyana sauran bayyanan ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button