Gwamnan Katsina Ya Bada Tallafi Wa Gajiyayyu 4000
A yau, Mai girma Gwamnan jihar katsina Dakta Dikko Umaru Radda ya bada tallafi wa mabukata gajiyayyu mutum dubu hudu a garin katsina.
Wanda suka samu Tallafin ya hada da matan da basu da abinyi da kuma Zaurawa. Tallafin ya biyo bayan wahala da ake sha sanadiyar cire tallafin mai da akayi watanni uku da suka wuce.
Gwamnan yayi hakan dan kawo sauki wa yan kasa da kuma dauki wa matsalar hauhawan farashi kayan abinci a jihar.