Labaran Yau

Gaskiyar Abinda Yafaru Tsakanin Acharaf Hakimi Da Tsohuwar Matarsa Hiba Abouk.

Acharaf Hakimi Da Tsohuwar Matar Shi Hiba Abouk, Gaskiyar Abunda Yafaru….

Hiba Abouk me shekaru 36, tsohuwar matar matashin ɗan ƙwallo Acharaf Hakimi mai shekaru 24, ta nemi kotu da ta raba dukiyar Acharaf a bata rabi sakamakon rabuwar da sukayi a 27 ga watan Maris.

Wani abu mai kama da almara shi ne bayan duba na tsanaki da kotun sauraron wannan ƙarar tayi ta gane Acharaf mugun faƙiri ne, hasalima ko kaso 80 na dukiyar da ake tunani ya na da ita ba tashi bace.

Duk wasu kadarorin sa Ya maka musu rijista da sunan mahaifiyar sa ne, hakan ya sa dokar turawa ta rabuwar aure 50/50 ba zatayi tasiri akanshi ba.

Mutane da yawa na tofa albarkacin bakinsu game da lamarin, yayin da waɗan su ke wa Acharaf kallan mai wayo, wa su kuma na yi mishi kallan tataccen azzalumi.

Ita kuwa Hiba tsohuwar matar ta shi, mutane na cewa ƴar san banza ce, idan ba haka ba tayaya daka auren ku shekara 2 sai ki nemi rabin dukiyar mutum, idan da kun kai shekara ashirin ya kenan?

Wasu kuwa sun ce dama haka tsarin rabuwar aure yake a turai, ko lokacin da Jaf Bezos ya rabu da matar shi Mackenzie haka yayi mata ruwan kuɗinnan wanda sai da alkadarin shi ya karye.

Amma wai meyasa Acharaf Hakimi da Hiba Abouk su ka rabu? Ga Dalili ⇓

A shekarar 2018, ƙarƙashin shahararriyar mujallar nan mai suna “Vogue”, Hiba Abouk ta je aiki birnin Madrid, anan ne suka haɗu da Acharaf, yayin da lokacin ya na taka leda da tsohon club ɗin sa na Real Madrid.

Tun da ga nan su ka bayyana wa juna ra’ayin kasencewa tare, sun cigaba da soyayya a ɓoye yayin da sai ashekarar 2020 tsaka da iftila’in Covid 19 suka yi auren sirri.

Bayan auren su Hiba ta haifi ƴaƴa guda biyu Amin da Na’im wanda su ne silar dole sai ta mallaki rabin dukiyar sa idan za su rabu.

A farkon shekarar nan Hiba tare da ƴaƴan ta, su ka tafi sharholiya Dubai, a yayin da shi kuma Acharaf mazantaka ta ci ƙarfin sa ya kasa jurewa har sai da ya shigo da karuwa gidan auren su domin ya yi amfani da ita.

Bawanda yasan da labarin sai ranar 25 ga Fabrairu a wannan shekarar lokacin da kotu ta zargi Acharaf da laifin “Fyaɗe” bayan karuwar nan ta kai ƙorafi.

Duk da ya musanta cewa shi ba fyaɗe yayi mata ba, amma ya yadda da ya shigar da ita gidansa kuma sunyi amfani da juna.

Tun lokacin ba aji ɗuriyar Hiba ba domin kare mijinta, kwatsam sai a 27 ga watan Maris ɗin da ya gabata, ashafinta na Instagram mai mabiya fiye da miliyan ɗaya akaga sanarwar rabuwar su.

Alokacin dama ta bayyana cewa suna hanyar kammala abin da ya kamata bayan rabuwa, wanda raba dukiyar shi na ciki, kwatsam bayan tayi zurfi gurin shan romo sai ta gano ashe barno gabas take.

Abin mamakin shine yanda mutane suke tunanin idan Hiba ta rasa kuɗin nan yaya zatayi da rayuwar ta?

Abunda ba su sani ba shine: Ita fa Hiba Abouk ƴar asalin ƙasar Tunisia ce, sun yi hijara ita da iyayen ta zuwa Spain da ƴan uwanta su Huɗu. Ta yi karatu mai zurfi a ɓangaren wasan kwaikwayo (Drama). Ta fi to afina finai kamar El Sindrome de Ulîses, La Isla De Los Nominados, da kuma shahararren fim ɗin ta’addancin nan wanda ta fito a Fatima mai suna El Principe.

A harkar wasan kwaikwayo darajarta ta kai yuro miliyan Uku da ɗigo ɗaya (£3.1 million). Hakan ke nuni ba ƙaramar kadara ce ba ita karan kanta. Sannan a shafin ta na Instagram ta na da mabiya 1.6 miliyan, wanda hakan ke nuna kamfanoni da yawa suna bata talla wanda akan haka ne ta haɗu da shi Acharaf ɗin.

Kuma sannan wai in banda ma abunku, ta ya ya mace mai masifar kyau da laɓɓa irin na hurul ain zata rasa wani hamshaƙin mijin, kai dai kawai Allah ya rabamu da talauci.

Usama Taheer Maheer

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button