Labaran YauNEWS

Shikenan Ba Ni da kowa – Cewar Mijin Da Aka Kashe Masa Mata Da Yara 4 A Jihar Anambra

Shikenan Ba Ni Da Kowa Cewar Mijin Da Aka Kashe Mata Mata Da Yara 4 A Anambra

Mijin mata mai ciki da ‘ya’yanta hudu da ‘yan IPOB suka kashe, mai suna Jubril Ahmed, yafito yayi jawabi yayinda ya ce har yanzu yana cikin rudani da tashin hankali,Jubril da ke aiki a matsayin mai gadi a jihar Anambra ya shaida wa Jaridar Daily Trust cewa matarsa tana gab da haihuwa a lokacin da abin ya faru.
Ya ce,

Yan Bindigan IPOB Din Sun harbe su ne a hanyar su ta dawo wa Anguwa

Suna Hanyar su ta dawowa gida bayan ta ziyar ci ‘yar uwarta da ke zaune a garin da ke kusa. Jikin su sanye da hijabi;wannan shine dalilin da yasa ‘yan bindigar suka far musu.
Har yanzu da nake magana ban gama dawowa cikin hayaci na ba, yanzu haka Yan sanda sun ba ni takardu da zan yi amfani da su wajen karbar gawarwakin su. Ina dakin da aka ajiye gawarwakin a yanzu haka, sun nemi in ba su N30,000 a matsayin kudin karban gawarwakin.
“Burina shi ne in kai gawarwakin zuwa garin Ganye da ke Jihar Adamawa,a can nake so a binne su, domin makabartar da ake rufe musulmai a nan Anambra ta cika.
Jibril ya bayyana sunan marigayiyar matarsa a matsayin Harira Jibril yar kimanin shekaru 32, sai ‘ya’yan su Fatima mai shekaru 9′ Khadijah7,Hadiza 5’ da Zaituna 2.
“Yanzu ba ni da kowa sun shafe ahalina tas.Ina cikin damuwa matuka, akwai bukatar gwamnati ta yi wani abu” inji 
Jibril.

An karbi gawarwakinsu Fatima Da Yayanta za a binne su a Anambra

Shugaban al’ummar Hausawa mazauna yankin Orunba ta Kudu, Sarki Kabiru Bakari, ya shaida wa Daily Trust cewa sun samu sun karbi gawarwakin a ranar Talata.
Sai dai ya ce daukan gawar zuwa garin Adamawa ba zai yiwu ba saboda rashin kula da gawarwakin da ba a yiba a dakin ajiyar gawa, hakan ne yasa gawarwakin baza su jure dogon tafiya ba.

Yanzu mun yanke shawarar kawai za a binne su a Awka a yau laraba. Ma’aikatan wurin ajiyan gawarwakin ba su kula da gawan sosai ba, ba su sa musu maganin hana rubewa ba; don haka ba za mu iya tafiya da gawarwakin ba saboda sun fara rubewa.

Kalli Bidiyo Dan Qasa Kadan ⇓

Domin Samun Labarai Ku Cigaba Da Shigowa Shafinmu Na Labaranyau A Koda Yaushe

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button