Shugabannin APC sun bada shawaran kar a bawa tsoffin gwamnoni mukamai
Dan Jam’iyyar APC Injinia Kailani Muhammad, ya bawa shugaban kasa Bola Tinubu shawaran kar ya zabi tsoffin gwamnoni kan mukaman gwamnati .
A bayanin shi, duka gwamnonin da ke zagaye da shugaban kasa Tinubu, yakamata ayi watsi dasu. Musamman wanda sukayi aiki dan kar a samu gashin kai na kananan hukumomi.
Ya kara da cewa harda tsoffin sanataoci da ministoti wanda basu tabuka aikin komai ba a gwamnati da ta gabata.
Khailani, wanda shi ne ciyaman na kasa na goyon bayan Tinubu kuma darakta janar na hadin kan APC, ya bayyana wa manema labarai cewa su goya wa tsohon gwamna AbdulAziz Yari baya na zama shugaban majalisan dattawa na goma.
“Wanda suke neman mukamai ba mutanen kirki bane kuma bamu bukatansu a mulki. Munata canza su daga wuri zuwa wuri na tsawon lokaci mai yawa. Shugaban kasa ya kamata ya kawo wasu wanda basu taba sata ba” A shawarar sa.
Cewar sa batun takarar shugabancin Majalisan dattawa, kailani ya ce Yari ba kawai dan takara bane daga arewa maso yamma, yankin da ta bawa shugaban kasa mafi yawan kuri’u a zaben da ta gabata.
Ya ce Yari yana daga cikin wanda sukafi aminta jam’iyyar APC, Kuma wanda yafi aiki tun daga Majalisan tarayya har zama gwamna jihar Zamfara.
A kan cire tallafin man fetur, kailani yace “wannan shine hukuncin da yakamata dan gwamnatin da ta gabata tayi ta daga ranar cirewa. Yanzu lokaci yayi dan kasa tayi abinda sauran kasashe sukeyi.”
Ya ce Najeriya a matsayin ta na mambar OPEC yakamata ta ji dadin siyar da mai da kuma cigaba na fannin ilimi, lafiya noma da kuma hanyoyi da sauransu.
Cewar sa cire tallafin nan fetur zai kawo gasa na kasuwanci kuma farashin man fetur zai fadi.
Daily trust ta rawaito