Labaran Yau

Sabon Zababben Dan Majalisan Tarayya Na Jalingo/Yorro/Zing Na Jam’iyyar PDP Ya..

Sabon zababben dan Majalisan tarayya na Jalingo/Yorro/Zing na jam’iyyar PDP Ya rasu

Samaila Maihanci, zababben dan Majalisan tarayya na goma wanda keh wakiltar Jalingo/Yorro/Zing a jam’iyyar PDP ya rasu.

Andeteran Irimiya, mai magana da yawun jam’iyyar PDP na jihar ya bayyana wa Hukumar labarai ta kasa a Jalingo.

A bayanin shi, maihanci matashin mutum ne wanda yaci zabe a inda jam’iyyar PDP bata kai labari . Ya mutu ne bayan ciwo na karamin lokaci ranar Asabar.

“Mun tashi da safe da mummunan labarin rasuwan sabon zababben dan Majalisan tarayya na yankin Jalingo/Yorro/zing na jihar Taraba.

“Samaila dan siyasa ne wanda akeso a koh ina wanda yakai da lashe zaben Majalisan tarayya a jam’iyyar PDP wanda kujerar bata iya ciwuwa wa jam’iyyar da jimawa.

“Jam’iyyar PDP ta na ta’aziyar wa yan uwansa da abokan sa, masu son shi da kuma yankin shi dan rashin shi’ ya ce.

Irimiya yayi addua wa mamacin dan samu cetuwar rai, kuma yayi addua wa yan uwansa dan samun hakuri jure rashin da sukayi.

Daily Nigeria ta rawaito

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button