Labaran Yau

Yan Garkuwa Da Mutane Sun Sake Dalibai Guda Hudu Na FGC Birnin

Yan garkuwa sun sake Dalibai hudu na FGC birnin Yauri

Hudu daga cikin dalibai goma sha daya da suka rage a hannun yan garkuwa na makarantan sakandare FGC birnin yauri jihar kebbi sun samu tsira.

Wanda aka sake akwai Faiza Ahmed, Bilha Musa, Hafsat Murtala da Rahama Abdullahi.

Salim ka, chairman na kwamitin daliban da akayi garkuwa da su, ya bayyana hakan wa manema labarai a birnin kebbi ran Asabar.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Yace, “ wata uku da suka gabata Mun nemi taimakon kudi dan mu samu mu dawo da yaran mu daga hannun yan garkuwa.

“Munyi amfani da kudaden da muka samu daga hannun jama’a da namu kudaden dan biya a sake mana wasu daga ciki guda hudu.

“A halin da ake ciki Mun biya Kuma an sake mana ‘ya’yan mu guda hudu daga hannun yan garkuwa.

“Farin cikin mu shine yaran guda hudu Suna gidan gwamnatin jihar kebbi cikin koshin lafiya”

Kaoje ya bayyana cewa iyayen dalibai bakwai daga ciki Suna daji, Suna sulhuntawa da yan garkuwan dan samun fitar yaransu daga hannun yan garkuwan.

Munira Bala Ngaski, uwar daya daga cikin yaran, ta nuna godiyan ta ga Allah don sake ‘yar da akayi.
Ya bayyana damuwanta da neman taimakon wanda suka kamata dan a samu a ceto sauran dalibai bakwai dake hannun yan garkuwa.

“Na shafi wata uku ban iya barci tunda Faiza Ahmed ta tsinci kanta a hannun yan garkuwa.

“Addua na shine sauran daliban Allah ya fidda su daga hannun yan garkuwan nan bada jimawa ba cikin koshin lafiya”

Dan sanda SP Nafi’u Abubakar ya kara bayyana hakan wa Hukumar labarai ta kasa.

Daily Nigeria ta rawaito, Labaranyau ta fassara zuwa harshen Hausa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button