Labaran Yau

Sabbin Masarautun Kano Sunzo Su Zauna Ne Martanin..

Sabbin Masarautun kano sunzo su zauna ne martanin da Ganduje yayi

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Yace sabbin masarautun Kano da ya kirkiro a mulkin sa sun zo su zauna ne.

A jawabin sa da yayi na ranan murnan yan kwadigo wanda akayi a filin kwallon Sani Abacha da ke Kano. Ganduje Yace Allah bare kawo wanda zai tarwatsa ba.

Gwamnan ya raba masarautar kashi biyar sannan ya sauke sarkin Kano na wannan lokacin Alhaji Muhammadu Sanusi.

A bidiyon da tayi yawo a shafin Sada zumunta satin da ya gabata, Sanata Rabiu Kwankwaso Shugaban jam’iyyar NNPP, Yace gwamnati mai jiran gado na Injinia Abba Kabir Yusuf, zai bincika dalilan cire Sunusi a sarauta.

Bisa hakan, bayan karasa bayanan sa a wajen bikin yan kwadigo, yace masarautun guda hudu an kirkiro su ne dan kawo hadin kai da zaman lafiya wa jama’a.

“Duk wanda yaje headquarters din masarautun zai fahimci an kawo ci gaba. Kuma mun kirkiro sabbin masarautun dan kawo hadin kai, cigaba da tarihi wanda zai dawo da martaban Al’adun masarautun. Mun kawo ne mu mutunta mutane da shiyoyi”.

“Inaso in jaddada muku masarautun mu na din din ne, sun zo su zauna ne, Duk wanda zai ne nemi ya rusa, Allah bare kawo shi jihar Kano ba. Mun kawo ne saboda jama’a da cigaba.

“Koh bama mulki muna addua Kuma zamu cigaba da Addua wa Allah ya kare masarautun mu. Nagode” cewar Ganduje.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button