Labaran Yau

Kampanin Layin Waya Sun Nemi A Ciresu Ciki Sabon..

Kampanin Layin waya sun nemi a ciresu ciki sabon doka

Masu kampanin layukan waya sun nemi Majalisan tarayya da ta ciresu cikin sabon dokokin da zata kirkiro ta gindayawa NITDA (Hukumar cigaban takanolagin zantarwa) karfin kula da lamarin su.

Masu kampanonin layukan a karkashin kungiyoyin su na masu lasisi sun bayyana wa kwamitin ICT da tsaron yanan gizo na Majalisan dattawa da na tarayya.

A bayanin su sun bayyana cewa in an bawa NITDA karfi, hakan zai sa su cikin matsa lamba dan kokarin kula da sharudan NCC da kuma na NITDA lokaci guda.

Dokar ta bayyana cewa za a bawa NITDA karfin kula da dokoki wanda ya shafi takanolajin zantarwa kuma tattalin arzikin dijital.

Idan Majalisan bata dakatar ba zai zama hukuma guda biyu suna kula da lamarin su akan abu guda zai kawo dagulewar su.

Kungiyar masu lasisi sunyi korafi kan cewa menene ke cikin takanolajin zantarwa da tattalin arzikin dijital.

Sun ce dokar ta bayyana tattalin arzikin dijital da kawo ci gaba wajen kirkire kirkiren abubuwa wanda ya danganci cigaban takanolaji wanda Kuma ita kanta takanolajin zantarwa ta danganci takanolajin dake kirkira da adana bayanai da musanya wa wajen amfani dasu, kamar bayanan kasuwanci, hira, hotuna da bidiyo.

Tun shekarar da ta gabata, jiga jigen ICT sunyi korafi cewa za a bawa NITDA karfin da ayyuka wanda NCC ke yi Kuma hakan kamata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button