Labaran Yau

Zamu Karbi Kujerar A Kotu Cewar Air Marshal Sadique

Zamu karbi kujerar a kotu cewar Air Marshal Sadique

Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar bauchi a zaben da ta gabata, Air Marshal Sadique Baba Abubakar (rtd) ya bayyana cewa zai karbo kujerar a kotu.

Hukumar zabe ta kasa, ta bayyana dan takarar jam’iyyar PDP, Bala Mohammed a matsayin zababben gwamna a jihar bauchi ranan 18 ga watan Maris, a zaben da ta gabata.

Bala ya samu kuri’u 525,280 ya lashe zaben, wanda ke biye dashi dan jam’iyyar APC Sadique Baba Abubakar yazo na biyu da kuri’u 432,272.

DOWNLOAD MP3

Sadique ya nemi kotu tayi bincike kan sakamakon zaben da ta gabata a Bauchi.

Ya bayyana wa yan jarida jiya a filin jirgin Abubakar Tafawa Balewa na Bauchi bayan ya iso Jihar. dan takarar jam’iyyar APC ya ce “Mun yarda da Allah da Kuma Kotun kasa dan zasu bamu kujerar mu wanda aka sace In shaa Allah”.

Ya kara da cewa yaci zabe Kuma zai bayyana hakan wa kotu.

DOWNLOAD ZIP

“Inaso in yarda da tsarin shari’a na Najeriya abun dogaro ne, Kuma na yarda cewa Duk abinda yaje ya dawo mune masu Nasara”. A cewar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button