Advertisements
Dalibai su fara duba sakamakon jarabawa ran Talata cewar Jamb
Hukumar Jamb ta bada shawara wa daliban da suka rubuta jarabawan na shekarar 2023, dasu fara duba sakamakon jarabawan ranan Talata.
Hakan tazo cikin bayanin babban jami’in Hukumar Jamb Dakta Fabian Benjamin wanda ya bayyana wa manema labarai a garin legas ranan Litinin.
A bayanin Benjamin, yace Hukumar ta batayi gaggawar fitar da sakamakon ba, Sai da akayi bincike, Aka tabbatar da komai kamin sakewa.
Advertisements
“Yayin da dalibai zasu duba sakamakon jarabawan su ran talata 2 ga mayu, Ana bada shawara wa Duk wanda suke fuskanci kalubale barasu ga sakamakon su ba Sai dai suga canjin rana nayin wani jarabawan.
“Duk daliban da suka rubuta jarabawan Ana bukatan su duba sakamakon kafin ranar 8ga watan mayu” a cewar sa.
Mista Benjamin yana kiran masu rubuta jarabawan su samu duba ranar da wurin jarabawan ran Alhamis koh ran jumma’a 4 koh 5 ga watan mayu, domin sanin ranar da lokacin jarabawan.
Jamb ta canza ranan Rubuta jarabawa wa wanda basu samu halin rubutawa ba.
Benjamin yace wanda aka tantance Kuma basu samu rubutawa ba, da wanda basu Zamu tantance war biometric ba, da wanda suka samu matsalar canjin bayanai.
“In zaku iya tunawa, Hukumar ta saka jarabawan ranan 25 ga watan Aprailu zuwa 2 ga watan mayu.
“Hukumar ta bayyana wa Najeriya cewa zata sa matakai na kiyaye duk wani badakala na jarabawa.
“An samu cimma buri sosai dan Hukumar bata fuskanci badakala da yawa, amma kuma an samu rashin kula na mutane yasa wasu basu rubuta jarabawan ba ranan farko.
“Cikin dalibai 1,586,765 wanda yakamata su rubuta jarabawan, akwai raran dalibai 80,166 suka rage basu rubuta ba” a cewar sa.
Advertisements