Matar Shararren Dan Kasuwa Na Jihar Katsina Dahiru Mangal Ta Rasu
Shahararren dan kasuwa, Alh Dahiru Mangal ya rasa matar sa Hajiya Aisha Dahiru Mangal.
Hajiya Aisha Daihuru Mangal ta rasu ne a wani asibiti da ke Abuja da yammacin ranar Asabar bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.
Wata majiya ta ce za a yi sallar jana’izarta a gidan Mangal, Kofar Guga, cikin birnin Katsina, da karfe 11 na safe ranar Lahadi.
Marigayi Hajiya A’isha ta rasu ta bar mijinta, ‘ya’yanta, da jikoki.
Wannan hasarar dai ita ce ta uku kai tsaye da ta shafi dan kasuwar a ‘yan kwanakin nan