Damagun ya zama zabebben jagoran PDP
Jam’iyar PDP ta zabi ma taimakin ciyaman dinta na yankin Arewa Amb. Umar Damagun ya yayi jagorancin jam’iyar, hakan yazo ne wa jam’iyar na yin biyayya wa kotu wanda ta takatar da Sen. Iyorchia Ayu a matsayin shugaban PDP ta kasa.
A yau talata, kwamitin kasa na jam’iyar tayi zama a Abuja akan odar da kotun Makurdi na jahar benue ta bayar dan gane da jagorancin jam’iyar a jiya 27 ga watan Uku.
Sakataren jam’iyar na kasa Debo Olugunagba ya bayyanar da hakan. Yace bayan dubi da lamarin gaba daya da jam’iyar tayi, sun yi la’akkari da nazari dan kawo lamuran cikin sauki Kuma suka zabi Amb.
Umar Damagun yayi shugaban ci daga yau Talata Ashirin da takwas ga watan maris har Zuwa lokacin da Kotu zata gama dashi.
A cewar sabon jagora mai rikon kwarya Amb. Damagun, Yace zaiyi zama ran laraba dan gano matsaloli dan gane da gudanarwa na jam’iyar PDP.
Yace Mista Ayu yazo yau da safe dan daukar wasu abubuwansa ne a offishinsu ba dan ya aiwatar da wasu ayyuka bane
Acikin wanda akayi zama dasu yau sun hada da National sakatare, Sam Anyawu, national youth leader muhammad Sulaiman da Usman bature wanda shine national organizing sakatare, da national legal adviser da national ma’aji, kamaruddeen Ajibade da Ahmed Muhammed.
Hukumar zabe ta Kasa INEC ta bayyana ranar karasa zaben Kebbi da Adamawa
Hukumar zabe ta bayyana Cewar zata gudanar da zaben gwamnoni wanda suka rage da yan majalisun jaha dana tarayya ran sha biyar ga watan hudu a fadin kasa gaba daya.
Kammalallun zaben gwamnoni guda Ashirin da shida (26), sanatoci dari da hudu (104), yan majalisan tarayya dari uku da ashirin da tara (329), yan majalisan jaha dari tara da talatin da biyar (935) INEC ta bayyana cin zaben su.