AddiniLabaran Yau

Falalar Lafazin Alhamdulillah

Falalar Lafazin Alhamdulillah

Malam yace lafazin Alhamdu karka rinka rabuwa dashi a bakin ka, Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yace fadin Alhamdulillahi idan anje filin Al-qiyama ba awu za’ayi ba? Annabi yace fadin Alhamdulillahi shi kadai ya kan cika mudun ka.

Wa subhanallahi wal hamdulillahi Annabi yace yakan cika abinda ya kai sama da kasa, sai yasa a karantarwa ta musulunci idan mutum ya tashi daga barci yace Alhamdulillahil ladhi ahyaana ba’ada ma amaatana wa ilahin nushuur,.اَلْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُورُ

DOWNLOAD ZIP/MP3

Idan yanayin gari baiyi dadi ba Alhamdulillahi Ala kulli haalin,

الْحَمْدُ لِلَّهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ

Idan yanayi yayi dadi Alhamdulillahi-ladhi bini’ matihi tatimmus-salihat الْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتُ,

Idan an ci abinci Alhamdulillahi-llazi at’amlani haza, wa razaqaniihi min ghairi haulin minni wa la quwwah

اَلْحَمْدُ لِلَّهِ الَّذِي أَطْعَمَنِي هَذَا، وَرَزَقَنِيهِ مِنْ غَيْرِ حَوْلٍ مِنِّي وَلَا قُوَّةٍ.  duk wanda yaci abinci yayi wannan adduar duk sabon Allah da yayi kamin cin abincin Allah ya yafe mishi. kuma yana daga cikin abinda yake jawo mutum ya samu yardan Allah, Allah yana yarda da bawa, yazama bawa ya samu yardan Allah, yaci yace Alhamdulillih ko ya sha abin sha yace Alhamdulillah.

Alhamdulillah ٱلْحَمْدُ لِلَّٰهِ ba karamar al’amari bane.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button