Addini

Amfanin Zuma Da Nono Daga Albani Zaria 

Amfanin Zuma Da Nono Daga Albani Zaria 

Zuma da nono asalin su abinci ne, Amma a cikin su suna da magani mai warkar da dan Adam game da wasu al’amura, bari kaji ko da kana ganin lafiya kake, kari ka samun lokaci kana Shan zuma zaka ga abinda zai faru dakai.

Yanzu inka dade Baka sha zuma ba, inka fita kayi kokari ka samu zuma ka sha, wani abin mamaki zuma ita ne zaka sha mai yawan da bazata maka illa ba.

Idan kasha ta, inda cututtuka ajikin ka, tana maganin wannan cututtuka zakaji zumar ta tattaro cutar a cikin ka wanda inka je bayan gida zaka fitar da shi ba irin wanda ka saba ba.

DOWNLOAD MP3

A cikin kashin ka ba zallan gurbatattun abinci bane kawai harda cututtuka da wasu ragowar datti da can yunkurin kashi baya fitar dashi. ruwa da kake sha bare iya wanko su ba. Misali ka samu kwalba mai datti sosai ka diba zuma ka zuba a cikin ta, inka zuba zumar ka samu ruwan dumi sai ka sa acikin zumar na cikin kwalbar sai ka rufe ka bata minti biyu zuwa minti biyar ka fara girgizawa kaga ikon Allah. Inka bude zakaga ta kankaro dayawa daga cikin dattin. Haka zuma takeyi wa cikin ka, idan kasha zuma kuma zumar bai kai yawan adadin dattin dake cikin ka daganan zaka fara gudawa, can sai kaji cikin ka ya kulle.

Shine ma’anar hadisin da muke ishara akai da Annabi SAW yace cikin dan uwanka yayi karya Amma Allah ya fadi gaskiya. Kayi wa cikin ka haka ka gani. Wato idan kasha ta, da gwalo da Kazan ta da dattin da ke cikin yafi karfin zumar to zata kankaro iya wadda zata iya kankaro wa sai ta fitar Saboda an hargitso cututtukan sai cututtukan su hadu sai cikin ya kulle, toh sake Shan zuma sai ta sake wankowa Sannan zakaji sai ka sake tsuguno kacigaba dasha har sai kaji cikin ya daina murdawa.

DOWNLOAD ZIP

A cikin Hadisi Annabi SAW Yace kurika Shan nonon saniya, domin nonon saniya na maganin kowani irin cuta. Saboda saniya tana cin kowani irin ganye na itatuwa. Wannan Hadisi sahihi ne tana sunani abu dawuda. Wannan Annabi SAW ne ya fadi. To ko kasan cewa yawan cin cututtuka idan an sha asalin nonon saniya ba wanda ya lalace ba Yana magani?

Da zaka Debo nonon saniya da habbatus sauda zai maka maganin cututtuka dayawa dake damun ainihin kirji. Da zaka nemo asalin nonon saniya ainihin mai kyan shi ka rinka diga mishi man zaitun kadan kana bawa danka ko yayanka mai cutan sikla da kaga ainihin waraka mai dinbin yawa. Wannan duk acikin sunnah ne na annabi SAW.

Sai yace wala kiyasu, ko gwadawa wannan likitoci binciken su bai kai ba.

Shafin mu ta labaranyau.com tana kokari wajen kawo fatahohin malamai dan amafanin Musulmai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button