Biography

Cikakken Tarihin Dauda Kahutu Rarara, Rayuwarsa, Daukakansa, Aikinsa, Siyasarsa, Arzikinsa, Hutunansa

Cikakken Tarihin Dauda Kahutu Rarara

Dauda Kahutu Rarara suna ne wanda ko ina ka shiga cikin masana’antar waka na Najeriya Musamman Arewacin sai kaji. Ya dau shekaru Yana waka kuma wakar ta taka rawar gani a kasar najeriya Musamman a siyasa ta kasa. A wannan shafi na labaranyau.com zamu baku cikakken bayani kan Tarihin rayuwa, daukaka, karatu, wakoki da kuma Arzikin Kahutu Rarara.

Cikakken Tarihin Dauda Kahutu Rarara 
Cikakken Tarihin Dauda Kahutu Rarara

Rayuwar Rarara

Rarara An haifeshi ranar 13 ga watan satumba shekarar 1986 ne a wani kauye da ake kira Kahutu da ke jihar katsina, Yayi karatun Addini wato na qurani a makarantar Almajiranci. Dauda kahutu ya kasance dan Najeriya kuma bahaushe musulmi.

Daukakar Rarara

Daukakar Rarara 
Daukakar Rarara

Rarara ya fara waka ne tun daga kasa, inda yake rera wakokin sa a wurare daban daban cikin jama’a a jihar Kano.

Yanayin tsara muryansa, sautin sa da kuma baitikan sa ya jawo hankalin mutane kansa dalilin haka ya samu daukaka a idon duniya.

Yana wakoki ne game da abubuwan da suka shafe mutane, kamar Al’ada, matsalolin da ke damun mutane da kuma siyasa wanda hakan ya bashi kakkausan murya a fadin kasar.

Ansanshi da baitukan hausa wanda ya hada da kidan zamani, hakan ya taimaka masa wajen fidda sabon sauti wa mutane. Yana da Albums daban daban da kuma wakoki daddaya da ya sake wanda mutane suke jin dadin su a ko ina a kasar.

Kuma Gudumawar da ya bayar a masana’antar waka ba abu ne boyayyiya ba. Hakan yasa Rarara yasamu karramawa daban daban Saboda jaddada shi a matsayin sa na shahararre mai babban murya a masana’antar waka a najeriya.

Siyasar Rarara

Siyasar Rarara 
Siyasar Rarara

Rarara ya samu shahara ne tun lokacin da akayi zaben shugaban kasa a Najeriya a shekarar 2015 inda ya mara wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari baya da wakoki masu kayatarwa da kuma nuna adawarsa wa Tsohon shugaban kasa mai ci na wannan lokaci Goodluck Ebele Jonathan a wakokin sa.

Saboda kaunar da akeyi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari hakan ya taimaka wajen son wakokin Rarara wanda mafi yawa a wannan lokacin wa Buhari ya rera. A shekarar 2020 Rarara yayi waka wa muhammadu Buhari inda ya nemi masoyan Buhari da su bashi naira dubu dubu dan sakar wakar wanda shi Rarara ya samu naira Miliyan Hamsin da bakwai Sannan ya fidda wakar.

Bayan nan ya wake yan Siyasar APC dayawa kamarsu Ganduje, Masari, Lolo, Gawuna, Airmarshal da sauransu. Ya wake wasu yan jam’iyar da bana APC ba kamar Shaaban sharada.

A zaben 2023 yayi wa shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu wakoki daban daban. Yayi wakoki tun kamin zabe, yayi lokacin zabe, yayi bayan ya ci zabe, yayi bayan rantsar da Bola Tinubu. Rarara ya kasance cikakken dan Jam’iyar APC ne mai kakkausar murya a waka game da siyasa.

Wakokin Rarara

Wakokin Rarara 
Wakokin Rarara

Dauda Kahutu Rarara yayi wakoki daban daban wanda suka samu shahara a masana’antar waka da kuma kasa najeriya baki daya. Wasu daga cikin wakokin sun hada da

 • Masu Gudu Su Gudu
 • Baba Buhari Dodar
 • Kwai cikin kaya
 • Saraki sai Allah
 • Dogara ne Sufikan mu
 • Buhari ya dawo
 • Baban Abba Ganduje
 • Malam Sha’aban
 • Ja gaba shine gaba
 • Kashim sauransu
 • Ganduje Shugaban party
 • Jagaba ya karbi kasa
 • Kashim sauransu
 • Uban Abba Zama daram
 • Kano ta Ganduje
 • Kudin Makamai
 • Jahata ce
 • Bauchi ta kaurace wa kaura
 • Lema Ta tsage
 • Lema ta sha kwaya
 • Jagaba sai ka shiga villa
 • Dagaske yake Dikko Radda
 • Uba Sani Ya haye
 • Gawuna saura kiris
 • Acikin Biyu
 • Aisha

Da sauransu.

Arzikin Rarara

Arzikin Rarara 
Arzikin Rarara

Dauda Kahutu Rarara yana arziki mai yawa wanda ya samu ta hanyoyin wakar siyasa da kuma manhajar wakoki.

Yana kasuwanci Amma har yanzu Muna aiki tukuru dan gano yawan arziki sa. Domin Rarara mutum ne mai matukar Arziki.

Hotunan Rarara

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button