AddiniLabaran Yau

Adduar Neman Ilimi Cikin Sauki

Adduar Neman Ilimi Cikin Sauki

Fatawa da malamai sukayi, a littafin I’ilamul muwakki eena An rabbil Aalameen na Shida, shafi na sittin da shida da bakwai da takwas zuwa da tara.

Ibnul Qayyim Al jawziyya Rahimatul lahi alaih Yayi magana akan abubuwan da ke sauwake haddan Qur’ani na addu’o’i, musamman muka sami tahqiqi na mashhur hasan salman, ya kawo rayuwar sa da malamin sa, Shaykhul Islam Rahimatullahi alaih na inda yake bayyana cewa babban abun da yake bada muhimmanci kan karatu da kuma karfin hada, shine kyautata Alaqa mutum tsakaninsa da Allah.

Yace wani lokaci zai yi kuskure dan karami sai ya fashe da kuka dan yana ganin yayi sabon Allah, sai ya tafi zuwa bayan gari, sai ya zauna lokaci mai tsawo yaki dawowa Yayi tuba ya kaskantar da kai ya tuba wa Allah, wani lokacin yakan tuba dai dai har so dubu yana tuba wa Allah. akan laifinda a yanzu baka dauka a matsayin laifi.

Amma su magabata duk kankantar sabon Allah yana tayar musu da hankali, meye dalili? muna kula da zunubin ne su kuma suna duba girman wanda ya haliccesu suke saba ma sa. kar ka duba kankanta zunubi, duba girman wanda ya halicceka ya maka duka ni’imomin da kake cikin su a yanzu. yace in yayi hakan ya dawo,duk abinda ya karanta wanda yake fargaban zaman su sai duk su zauna in ya karanta.

kuma karatun da yake yi na awanni kamin ya fahimta cikin karamin lokaci sai ya fahimta,
In yayi wata wajen fahimtar wani sharhi wani lokacin cikin kwana daya ko kwana kadan sai ya fahimci abinda yake neman fahimta in ya kaskantar da kanshi ya tuba, kyautata Alaqa da ubangiji yafi muhimmanci wajen neman sauki wajen karatu da hadda.

Akwai Addu’o’i, malamai suka ce ba a samu wata addua guda daga ka karanta wanda in ka karanta zaka samu fahimta da saukin hadda ba, sai dai ayoyi da hadisai da ke da alaqa da neman fahimta.

Ibnul Qayyim ya kawo misalai na magabata da dama ta inda suke zama suke addua sai kaga Allah ya saukake musu abu, ya ce magabatan
mu na salaf daga cikin abinda suke karantawa idan suna so Allah ya bude musu kirjin dan su fahimci karatu suna yawan maimaita ”Laa ilma lana illa maa allamtana inna ka anta alimul hakim ko rabbi zidini ilma” Allah ka kara min ilimi, addua ce maimuhimmanci da fiyayyen halitta ya roki Allah karin ilimi kuma Qur’ani ya hakaito mana wannan.

Imamu Maalik ya bayyana cewa dabi’arsa shi yana maimaita Mashaa Allah laquwwata illa billah, abinda Allah yaso Babu karfi babu dabara sai ga Allah
neman ilimin nan bakada karfi ko dabara sai abinda AllAH ya baka. Imaamu Maalik yana yawaita hakan kuma yayi aduan Allah ya bashi ilimi mai albarka.
wannan shine kadan daga cikin misalai daga maluma. Allah ya bamu ilimi mai Yawa mai Albarka.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button