Farashin Kayayyaki Yayi Tashin Goron Zabi A Amurka
Hauhawar farashin kayayyaki a Amurka na kara tsananta a baya bayan nan, inda kudin shigar jama’a ke kara raguwa. Kuma mummunan tasirin hauhawar farashin ya fi shafar masu karancin kudin shiga fiye da masu hannu da shuni.
Karuwar farashin kayayyaki kamar na abinci da gas na kara matsi kan kudin shigar Amurkawa masu karancin kudin shiga.
Ko a ranar 5 ga wata, babban jami’in babban bankin kasar Lyle Brainard, ya bayyana a Minneapolis, yayin taron binciken harkokin kudi na bazarar 2022 cewa, iyalai masu karamin karfi na kashe kaso 77 cikin dari na kudin shigarsu kan bukatun yau da kullum, yayin da masu hannu da shuni ke kashe kaso 31 cikin dari kacal. Baya ga haka, wani rahoton da reshen bankin a Cleveland ya fitar a baya bayan nan, ya bayyana cewa, Amurkawan da suka samu karin kaso 7 kan abun da suke samu a bara ne kadai za su iya ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya.
Shi kuwa shugaban bankin reshen Philadelpia, Patrick Haney ya ce, rashin manufofin kudi masu tsauri da tsaikon da aka samu a tsarin samar da kayayyaki ne tushen tabarbarewar hauhawar farashin.