Doguwa ya lashe zaben majalisan tarayya na yankin tudun wada/doguwa a jihar kano
Hukumar zabe ta INEC ta bayyana majority leader na majalisan tarayya, Alhassan Doguwa wanda yaci zaben majalisa Na doguwa/tudunwada a jihar Kano.
Zaben da aka sakeyi yazo da sakamakon nasara wa dan majalisa wanda akayi ran asabar.
Jami’in hukumar zabe, farfesa Sani Ibrahim ya bayyana jam’iyyar APC ta samu kuri’u 41,573. Wanda ya biyo shi a baya jam’iyyar NNPP ta samu 34,831, Sai Kuma jam’iyyar PDP ta samu 211.
Rajistan zabe ta nuna mutane 227,912 akayi wa rajista Kuma mutane 80,933 aka tantance.