Labaran Yau

Hukumar Zabe Ta Janye Bayyana Aisha Binani A Matsayin Gwamna

Hukumar zabe ta janye bayyana binani a matsayin gwamna

Hukumar zabe ta Kasa INEC ta bayyana Aisha Dahiru, wanda aka fi Sani da binani a matsayin wanda ta lashe zaben da akayi jiya ran asabar a jihar Adamawa.

Hada sakamakon zaben yana cikin gudana kamin a gama hada sakamakon zaben.

Sakamakon zaben na kananan hukumomi 10 a cikin 20 an kammala, wanda hakan yasa aka daga Sai 11 da safe a cigaba da hada kan sakamakon zaben.

DOWNLOAD HERE

Amma zuwa karfe 10 na safe, kwamishinan zabe na jihar, Hudu Ari, yazo shi kadai ba tare da meh bayyana sakamakon zaben ba, a nan ya bayyana Binani a wanda ta lashe zaben.

Bayan dokar zabe ta nuna cewa kwamishinan baya iya bayyana sakamakon zabe.

Daily Nigeria ta rawaito cewa Gwamna Ahmad Fintiri na jam’iyyar PDP yana gaba a kananan hukumomi 7 cikin goma Kamin aka sanar da binani ta lashe zaben.

DOWNLOAD MP3 HERE

Wasu daga jam’iyyar PDP sun nuna rashin yarda da sukayi na bayyana sakamakon Kuma ba zababben wanda yakamata ya bayyana sakamakon ya bayyana ba.

Hukumar zabe ta bukaci karin jami’an tsaro a jihar Adamawa

Hukumar zabe ta nemi karin jami’an tsaro wa kwamishinan su guda biyu da sauran jami’un su wajen zaben da aka sake na gwamna a jihar Adamawa.

Hukumar ta bayyana hakan a ta muryan kwamishinan su ta kasa na zantarwa da wayar da kai akan zabe, Festus Okoye a ABUJA ran lahadi.

Ita hukumar ta tsayar da bayyana sakamakon zaben wanda kwamishinan zabe na jiha Hudu Yunusa Ari yayi a tsakiyar hada sakamakon zabe. Hukumar ta bayyana hakan baya tsari Kuma hakan bai yiwu ba.

Okoye, yace Hukumar ta damu da tozarcin da akeyiwa jami’an su Kuma sun nuna rashin jindadin su da Kuma yin gargadi dan a daina.

Hukumar ta damu matuka da cin mutuncin da ake wa kwamishinan su guda biyu wanda suka kawo dan samu ayi zabe cikin kwanciyan hankali da Gaskiya.

Suna neman jami’an tsaro da su sama musu tsaro meh inganci Kuma kar su bar wani abu ya faru dasu.

Duka jami’an zaben yakamata a barsu suyi aikin su yanda ya dace. Da Kuma yanda Hukumar ta bukaci suyi, A cewar mista Okoye.

Ya kara da cewa Hukumar zabe barata lamunci wani abun rashin doka da cin zarafin jami’an su ba a cikin yanayi na zabe ba.

Okoye yace bayyana sakamakon zaben da akayi bashi bane wanda Hukumar ta sani ba. Hukumar barata yi amfani da wannan sakamakon da kwamishinan jiha ta zabe Ari yayi ba dan ba hurumin sa bane.

Hada sakamakon zaben ta tsaya, yayin da Hukumar ta kiraye wanda zasu bayyana sakamakon da sauran jami’an su dawo babban ofishin Hukumar a Abuja.

Daily Nigeria ta rawaito.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button