Orji kalu ya ziyarci Buhari don neman goyon bayan zama shugaban Sanatoci
Shugaban kasa Muhammadu buhari ya hadu da sanata orji kalu a bayan fage a fadar shugaban kasa ran talata.
Mista orji yayi hira da manema labarai ya bayyana cewa fadawa shugaban kasa buhari akan Niyyansa na takaran shugaban majalisan sanatoci.
A fadan shi, idan mukamin an kai kudu ta gabas a jam’Iyar APC, hakan zai kawo kwanciyan hankali a kasa gaba daya.
Ya kasance gwamna na zama daya a jihar Abia, Duk da hakan ya tabbatar da yankin basu zabi Sanata Bola Ahmed tinubu ba, a zaben shugaban kasa da ta gabata. In zai samu ya zama shugaban majalisan sanatoci hakan zai kawo yelwantuwar zaman lafiya a kasar.
Ya qara da bawa Buhari shawaran karban lambar amintattu na jam’Iyar APC saboda gaskiyar sa dan su samu wanda zai na musu sulhu in an samu Matsala a jam’Iyar.
A cewar sa jam’Iyar ta hadu da matsaloli na rarrabuwan kai Kamin zabe. Saka bakin Shugaba buhari ya kawo sa’ida ta samun sulhu a tsakanin su.
Ya kara da bawa shugaba buhari shawaran kar yayi ritaya a siyasa dan yana da muhimmanci da jagorancin jam’Iyar ta su.
Tinubu ya zabi Bagudu da tsohon kwamishinan kudi ta jihar legas a kwamitin shirye-shiryen gudanar da bawa karagar mulki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zabi Boss Mustapha ya jagoranci kwamitin shirye shirye da tsare-tsare wajen gudanar da bada karagar mulki ga sabon shugaban kasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu, wanda za ayi ranan Ashirin da Tara ga watan mayun shekara ta dubu biyu da uku.