Labaran YauNEWS

Anyi Asarar Rayuka A Abuja – Rikici

Anyi Asarar Rayuka A Abuja – Rikici

 

Akalla mutane biyar ne aka ruwaito an kashe tare da kona gidaje a wani rikici da ya barke tsakanin Yan kasuwa da Yan acaba a unguwar Dei-Dei dake babban birnin tarayya, Abuja.

Wani mazaunin garin ya shaida wa Tashar Channels cewa, hatsaniyar ta kaure ne lokacin da wani dan acaba ya yi hadari.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Mutane biyar da na sani an kashe su a wannan lamarin. Mun yi ta kiraye-kiraye ga jami’an tsaro su kawo dauki amma basu Samu damar zuwa ba,” inji mazaunin garin wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Muna matukar tsoro kan wannan rikicin ya karkata zuwa ga na kabilanci.”

Ba za mu iya tantance adadin mutanen da suka mutu ba, amma daya daga cikin wadanda abin ya shafa ya tabbatar da cewa an kona gidansa.” Inji wakilin Tashar Channels.

An ce Yan kasuwar su suka fara kai hari ga dan acaban kan zarginsa da sanadiyyar mutuwar fasinjan.

Rahotanni sun ce abokan aikin dan acaban, sai suka yi yunkurin kubutar da shi daga hannun Yan Kasuwan, Wanda hakan ya kara damalmala rkicin.

Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button