Labaran Yau

Gwamnatin Tinubu Ta Dau Niyyan Bada Ilimi Wa Yara Mata – Shettima

Gwamnatin Tinubu Ta Dau Niyyan Bada Ilimi Wa Yara Mata – Shettima

Mataimakin shugaban kasa yace gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ta dau niyyan bada ilimi da karfafawa wa mata.

Tinubu
Tinubu

Mataimakin shugaban kasan ya fadi hakan ranar laraba yayin da amshi ziyarar Majalisan dinkin duniya wanda mataimakin sakatare janar da Kuma shugaban Majalisan dinkin duniya kan Sustainable Development group, Amina J Mohammed.

Ta samu rakiyar Malala Fund, wanda Malala Yousafzai da wasu jami’un suka halarta.

DOWNLOAD ZIP/MP3

Ya tabbatar wa Malala fund yunkurin Gwamnatin Tarayya da tayi na hadin kai dasu dan cigaban yan Najeriya.

A Jawabin daban daban Amina Mohammed da Malala Yousafzai, sun yabawa Gwamnatin Tarayya wajen yunkurin ma buri na 4 da 5 na sustainable development goals na Majalisan dinkin duniya, yayin da Gwamnatin take kokari wajen bada karfafawa gwiwa wa mace da Kuma bada ilimi wa mata a kasar.

Maganar da akayi da manema labarai bayan zaman da sukayi a bayan kofa, Malala Yar kasar Pakistan ta kasance mai neman yancin mata kan ilimi, wanda ta samu karramawa na 2014 Nobel Peace Prize, tace Tana Najeriya dan tayi murnan haihuwan ta na cika shekara 26, ta ce Tana yawo a fadin duniya Tana haduwa da mata daga kasashe daban daban wajen bayyana matsalolin da mata suka fuskanta tun bayan jawabin ta a Majalisan dinkin duniya lokacin Tana da shekara 16.

Ta kara da cewa taje makarantu Kuma ta hadu da masu neman yancin ilimin mata a Abuja da Jihar Borno, ta jaddada amfanin ilimin mata wanda zai kawo cigaban kasa Najeriya.

Cikin mambobin da suka ziyarci Mataimakin shugaban kasan sun hada da, Mista Mathias Schmale Resident Cordinator na Majalisan dinkin duniya a Najeriya, Ms Annemarie Hou na ofishin hadakaiya Ta Majalisan dinkin duniya, maitaimaka wa DSG na musamman Hadiza Elayo, da Mista ziauddin yousafzai da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button