Tsarin Neman Aure A Addini Daga Prof. Isa Ali Pantami
Yaya ake tafiyar da neman aure mataki bayan mataki. Neman aure a sharia abu ne mai sauki. Abu na farko da mutum zaiyi in zai fara neman aure shine ya ga matan. Sai ya tashi takanas zuwa wajen waliyinta ko da kansa ko yaje da waninsa, kuma ku duba wasu al’adan wanda basuci karo da addini ba dan wasu al’adan basu yarda kaje da kanka ba, wai hakan rashin kunya ne, toh sai ya tura wakilin sa mahaifinshi koh dan uwansa.
Kamar saudiyya kai kana zuwa da kanka, zaka iya zuwa da babanka ko abokinka domin neman aurenta ba abu ne mai laifi ba a wannan kasashe. Har za a ce waye zai karbi auren miji ya gyara hula yace ganin ya karbi abun shi dan Kar a samu matsala.
Nabiyu bada izini dan ka kalli ita yar, Almugheeratu bn Shu’uba RA ya daura niyyar zai yi aure zai auri wata yarinya, sai Annabi SAW yake cewa kaje ka kalleta kallan ta shi dawwamar da soyayya a tsakanin ku. Asalin kauna, Yakamata ka kalleta kasan tayi ko batayi ba. Abinda kake bukata wani bashi yake bukata ba. Wani inka gayyace shi Shan ruwa sai yace Yana son kunu da kosai. Wani inka gayyace shi ka bashi kunu da kosai zai ce ka wulakanta shi. Yana bukatan ka kawo masa kaji an yanka, wani kuma doya da miya yake so. Abinda wani yakeso wani baya bukata.
Sai yasa a shariah ake so mutum ya kalli mace, kuma bawai tasaka hijabi ko niqabi kamar zata je kiyamul layli, ba haka ake ba a shariah. Zata saka kaya ta rufe jikinta Amma ta bayyana wuraren da ya halatta idan tana wanke wanke ko shara a cikin gida a gani. Amma kuma Kar a wuce gona da iri. Sai tazo ta wuce a gabanka kaga tafiyar ta da sauransu. Wani nason baka wani nason fara, wani nason mai tsawo wani nason mara tsawo wani nason mai kiba wani nason mara kiba, Kowa da abinda yakeso da kuma yake bukata. Toh itama mace tana da zabi, akwai abinda take bukata in kana da shi tace kayi in baka dashi tace bakayi ba. Wata zata ce mai gemu nake bukata. Bawai sharadi ne kai kadai aka baka ka darje ba, itama an bata ta darje kaima sai kayi tafiya ta gani saboda aure ana gina ta ne kan kauna bawai kawai kace astagfirullah baraka gani ba wani yaje ya gani maka ?
In tayi sai kaje ayi magana sai a wakilce ka, idan kaga ta maka akwai matakai da ake bi kala kala in mutum ya ga tayi. Na uku akwai muwafaqa wato ka mata ta maka, muwafaqa yana nufin compatibility, wato kun dace da juna, sai ku danyi maganganu sai ka gane ita ma ta gane yadda kake, Saboda har magana akwai irin wanda mutum ke bukata, in irin muryanta ya maka haka itama innaka muryan ya mata toh shikenan. Saboda akwai abinda ga namiji ado ne a wajenta muni haka mace ma abinda ado ne a wajen shi muni ne.
Kalli Bidiyon A Nan Domin Samun Karin Bayani