Tsakaninmu Da Wanda Suka Cutar Damu – Maryam Abacha
Uwargidan tsohon shugaban kasa, Dakta Maryam Sani Abacha, ta ce lokaci ya yi da za ta yafe wa duk wanda ya zalumce ta da danginta, ta kara da cewa babu wani abu da wani zai yi mata na zalumci da ba za ta iya kawar da kai akan shi ba.
Da take jawabi yayin bikin cikarta shekaru 75 da haihuwa a Abuja ranar Alhamis, Maryam Abacha ta bukaci jama’a da su rungumi yafewa juna domin hadin kai da ci gaban mu.
Ta ce; “Daya daga cikin abubuwa masu kyau a rayuwa shine mutane su rungumi ruhin gafara a tsakaninsu. Ya kamata mutane su koyi yadda ake gafarta wa juna. Gafara tana da matukar mahimmanci kamar yadda aka jaddada ta a cikin harsuna da addinai daban-daban. Gafara tana inganta zaman lafiya da sauran alfanu masu yawa na zamantakewa.