Labaran Yau

Wani Matashi Ya Bayyana Soyayyarsa Wanda Tafi Na Rakiya Moussa Poussi Rikitarwa Da Abun Tausayi

Wani bawan Allah ya bayyana ciwon soyayyarsa bayan na Rakiya Mousa Pousi

Ana wata ga wata kamar yanda soyayyar Rakiya Moussa Poussi ya rikirkita kafafen zumunta wani dan saurayi yafito shima yayi tsokaci dangane da soyayyarsa.

Bawan Allah dai meh suna Khamis Basheer Bako Ayagi ya bayyana hakan shafin sada zumunta bayan labarin Rakiya Mousa ya karada ko Ina.

Khamis Cewa Yayi:

Ba Rakiya Ce Kadai Ta Faɗa Jarrabawar Soyayya Ba, Nima Na Faɗa Har Saida Ta Kai An Kwantar Dani Asibiti

Ban so yin wannan maganar ba, saboda ni ba na zancen soyayya, saboda gudun yin rashin kunya a bainar jama’a tunda akwai iyaye na a sahar, shiyasa ban taɓa yi ko bada labari ba.

Idan ana wani zancen shiru kawai ake yi, na rantse da Allah shekara ɗaya da rabi da ta wuce ban zaci zan rayu ba, duk dalilin So, domin fadeelat ta samu wanda zata Aura wanda ba niba

Idan da a ce zan bada labarin soyayya ta da Fadeela ( rayuwa ta) to’ da, da yawan masu karatu sai sun zubar min da hawaye saboda ciwo, na so Fadeela son da ban yi wa kaina ba ma, ina jinta a rai na har gobe ba kuma zan daina ba, koda ace na daina sai dai idan ban tuno ta ko ta kirawoni ba!

So bala’i ne!

Wannan hoton na ƙasa shine lokacin da, aka kai ni asibiti domin samun kulawar gaggawa bayan mahaifin Fadila ya kira ni a waya zuwa gidansa ya sanar da ni cewa jiya ya karbi kudin auren Fadila daga hannun wani.

Muna matuƙar ƙaunar juna har gobe. Kuma ban daina kallon mahaifinta a matsayin uba ba har gobe.

Asalin Wanda Ya juyawa Rukaiya Mousa baya a soyayya ya bayyana

Kamar yanda labarin Rakiya Mousa ya riskemu jarumar dai yar kasar nijar ce wanda ta shahara a kannywood wajen yin fina finan hausa, waka da rawa.

Jaruman ta kasance mawakiya wanda ta bayyana cewa ta gada ne wajen mahaifinta wanda shima ya shahara wajen yin waka da hausa da yaren nasu na kasar nijar a shekarun baya

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button