Duk wadanda suka yi nasara a zaben bana babu wanda nake tausayawa kamar Engr Abba Kabir Yusuf saboda dalilai kamar haka
Dr. Sheriff Almuhajir yafito shafin yada zumunta yanda yake jawabi akan mahangansa da kuma tausayawarsa gameda zabebben gwamnan Kano wato Abba Gida Gida.
Dr Sheriff ya rubuto dalilai guda 6 kwarara wanda muka kawo muku su anan Shafin Jaridar Labaranyau Blog.
Ga dalilansa na tausayawa zabeben gwamnan Kano ⇓
1. Biyan bukatun maigidan shi da ya tsaya ma shi har ya zama Gomna da kuma bukatun al’ummar da suka zabe shi ya yi nasara
2. Biyan bukatun jama’ah ma su kyautata zato da burin su, da kuma lura da karancin kudaden da Gomnatoci ke samu a yanzu
3. Biyan bashin da Gomnatin baya ta ci da kuma yin ayyukan raya kasa
4. Gina sabuwar Gomnati da juya akalar da Gomnatin baya ta sanya a gaba
5. Biyan bukatun matasa na kai su kasashen waje karatu kamar yadda Gomnatin su ta yi a baya, lura da tashin farashin dala da tsadar rayuwa a duk duniya
6. Daidaitawa tsakanin bukatun maigidan shi da yan kasuwa musamman wadanda suka sayi filaye suka kashe dukiya wajen gine-gine, suka bude shaguna da kasuwani suka baiwa mutane wajen sana’o’i. Da sauran abubuwa da dama.
Daga karshe Dr yakara da cewa
“Amma dai ala kulli halin muna taya shi addu’a da fatan Allah ya bashi ikon sauke wannan nauye-nauye”.
Shugaba buhari ya samu amincewar majalisan tarayya kan kirkiro sabbin wuraren shakatawa na kasa
Majalisan tarayya Ran Alhamis ta Amincewa neman kirkiro sabbin wajen shakawa na kasa guda goma.
Hakan yazo da mabiyi da tallafi Wanda Ado doguwa shugaba a majalisan yayi a Abuja.