Shugaba buhari ya samu amincewar majalisan tarayya kan kirkiro sabbin wuraren shakatawa na kasa
Majalisan tarayya Ran Alhamis ta Amincewa neman kirkiro sabbin wajen shakawa na kasa guda goma.
Hakan yazo da mabiyi da tallafi Wanda Ado doguwa shugaba a majalisan yayi a Abuja.
Majalisan dattawa ta saka hannu dan amincewa da neman da shugaba buhari keyi kan kirkiro da wajen shakatawan ran talata.
Dan majalisa Malam doguwa yace buhari a nowamba sha shida a shekaran da ta gabata akan kirkiran wajen shakatawa goma.
Yace hakan yazo daidai da dokan wajen shakatawa, wanda a rubuce shugaba buhari ya turo majalisan dan neman yardansu.
A hakan, shugaba buhari da majalisan tarayya zasu bayyana wurare goma a fadin kasa wanda za’a maida su wuraren shakatawa ta kasa.
Yace hakan zai sa a bayyana, kuma a kimanta wuraren, da doka na wuraren shakatawa na kasa.
Sabbin wuraren shakatawa na kasa goma da za a kirkiro sun hada da: Allawa game reserve na jihar neja, Apoi game reserve na jihar bayelsa da Edumedum a jihar bayelsa.
Sauran kuma ya shafi Falgore game reserve na jihar Kano, baturiya wetland game reserve na jihar jigawa, Kampe forest reserve na jihar kwara, kogo forest reserve na katsina, da marhai forest reserve na jihar Nasarawa.
Akwai Oba hill forest reserve na jihar Osun, da kuma Pandam forest reserve na jihar Filato.