Labaran YauNEWS

Da CBN Da Shugabannin Najeriya Zasu San Asarar Da Zaa Tafka – Falalu A Dorayi

Sannanen jarumin Kannywood, Darekta kuma produsa da akafi sani da Falalu a Dorayi ya jawo hankalin CBN da Gwamnatin Najeriya akan wa’adin chanjin kudin

Ga abinda Falalu A Dorayi a daura ashafinsa na Facebook ⇓

Da CBN za tai duba da irin asara da mutane zasu tabka da an danyi kari akan wa’adin da aka bayar na canjin kudin nan. Da yawan mutane kusan har dare suke kaiwa a layin saka tsohon kudi su karbi sabo, mutanen karkara kuwa mafi yawan su ba su ma da Asusun ajiya a banki a haka suke kasuwanci da kudi a hannu.

Kuma maganar gaskiya Hanyar fadar sakon canja kudin da CBN tayi kadan, sannan wa’adin yayi kadan.

Ni na dauka in ana cikin matsin tattalin arziki, Sassaukar mafita ake nemawa al’umma, ba kokarin jefa su cikin ukuba ba, bafa karamar asara za’a yi ba.

Ukuba irin wannan tana bukatar duba na tausayi da jinkai, domin kauda kai da kin kara lokacin, kai tsaye ya nuna Gwamnati ta juya baya ga al’ummar da suka zabe ta.

Kuma irin wannan halin shi ke haihuwar sababbin matsaloli, kuma ya jefa iyalai da yawa cikin talauci, wasu ma daga hakan sun haukace kenan.

A shekarun baya a lokacin da President Muhammad buhari Yana mulkin soja, anyi canjin nan an bamu labarin irin masifar da mutane suka shiga. Sannan ya faru kwanannan a Kasar Indian, har Yanzu mutanen kasar basu dawo hayyacinsu ba.

Shugabanni su duba masalahar masu rauni cikin Al’ummarsu Shine adalci.

Meh zakace dangane da chanjin kudin nan da akayi?

 

DOWNLOAD ZIP/MP3

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button