
Raheem Sterling Ya Kwaci Chelsea Da Kwallo 2 Da Assist 1 A Stanford Bridge
Bayan wasa biyu da Chelsea suka buga, wadda aka shasu daya, sukayi draw a daya, sunci wasan su na uku. Mauricio Pochettino wato sabon kocin yayi nasara na farko a matsayin kocin Chelsea.

Chelsea sun bude cin kwallo a minti 17 na farkon wasa, inda Sterling ya shigo da kwallon a gefen dama sannan ya buga kwallon a kasa har cikin ragar Luton, kwallon ta wuce kowa har gola be iya tabawa bah.
A minti 68 Raheem Sterling ya sake jefa kwallo a ragar Luton, wadda Malo Gusto ya yanko kwallon a kasa Sterling kuma ya sameta a dai-dai ya buga ta cikin ragar Luton.

Nicholas Jackson yaci kwallon sa na farko a Chelsea, wadda Sterling ya buga masa kwallon a kasa da karfi, shikuma ya shigar da kwallon cikin ragar Luton.

Chelsea sun tafi da maki 3 a wasan, Luton Town kuma sun koma gida babu maki koh daya. Luton Town sunyi kokarin kai hare-haren cin kwallo amma basu samu nasarar shigar da kwallo koh daya cikin ragar Chelsea bah.