Ko Meyasa Samaruka Ke Guduwa Daga Wajen Yemmata Lokacin Ramadana
A Yau zamuyi Tsokaci ne game da samarin da suke guduwa da azumi su dawo bayan Sallah.
Akasarin ‘Yan mata na kokawa dangane da wannan al’amari wanda dalilin hakan ke sa wa su ga gazawar samarin ta wannan fanni, musamman ta yadda basa iya yi wa ‘yan matan nasu kyauta. Yayin da wasu kuma suke ganin rashin dacewar hakan muddin kuwa an gina soyayyar bisa gaskiya da amana. Sai dai kuma ta bangaren su samarin wasu na ganin hakan shi ne dai-dai musamman yadda wasu ‘yan matan suke yawaita roko da zarar watan azumi ya gabato, ko kuma ‘yan matan da suka guje musu kafin azumi, sai su fara kokarin dawo wa da zarar azumin ya gabato, wanda dalilin hakan ke sa mazan gudu wa. Wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin matasan inda suka bayyana nasu dalilin da yasa Samarin suke guduwa, Shin ko ‘yan Matan za su iya ci gaba da soyayya da samarin da suka gudu suka dawo bayan sallah?, ga dai ra’ayoyin nasu kamar haka:
A cewar wata Bududurwa, Saurayi yana guduwa ne saboda tun farko da ma ba don Allah yake sonki ba ya yi wasa da hankalinki ne dana iyayenki so da yawa irinsu ne ke wannan tafiyar amma idan ana soyayya domin Allah ka yi mata bayanin halin da kake ciki za ta fahimta tun da ba dole a ka ce Ramadan Basket din ba, amma azumi na zuwa sai ki ga an nemi abin da za ku yi fada dan ba zai iya baki abin shi ba. Ni wadannan ina saka su ma a layin marowata ko aure a kayi dan irinsu ne masu lallabarki ya kwashe lefenki ya siyar. A’a! ba zan iya ci gaba da soyayya da wanda ya gudu ya dawo ba, ai idan a ka yi gaba ba a bukatar a dawo baya ci gaba a ke so, ba ci baya ba, ta yi wu haduwa ta da kai tun asali ba alkhairi bane, ka zo kuma ka tafi saboda karamin dalili to kin ga babu maganar dawowa. Shawara ga masu wannan hali aji tsoron Allah, idan an san ba domin Allah a ke kaunar budurwa ba a barta mai kaunarta ya zo gare ta, ba sai ka gama bata mata lokaci ba da karairayinka da ba su da makama sannan daga baya ka ce za ka dawo, kana da kanwa kila ma kana da mata da diya sai ka kwatanta idan a ka yi wa diyarka yadda za ka ji, kuma a ce wacce ka fi so a cikin diyarka din, mu gyara dan Allah wassalam.