Shugaban kasa Tinubu Ya Nada Sabbin Hafsoshin Tsaro Na Kasa
Shugaban kasa Bola Tinubu Ya sauke hafsoshin tsaron na kasa, Yayin da ya Mai da gurbinsu da zaben sabbi a madadin su.
Sun hada da mai bada shawaran tsaro na kasa, hafsoshin soji, Insufeto janar na yan sanda, da kwantrola janar na kwastam.
Willie Bassy, Daraktan bayani na ofishin sakatare Gwamnatin Tarayya, ya bayyana hakan ranan litinin a Abuja.
A bayanin Bassy, Shugaban kasan ya mai da gurbin wanda yayi wa murabus.
Wanda aka zaba sun hada da, Malam Nuhu Ribadu, Mai bada shawaran tsaro na kasa, major janar Christopher Musa hafsin tsaro, major janar Taufeeq Lagbaja hafsin sojin kasa, Rear Admiral EA Ogalla hafsin sojin ruwa, da kuma AVM H.B Abubakar hafsin sojin Sama.
Wasu daga ciki sun hada da DIG Kayode Egbetokun mai rikon kwaryar insufeto janar na yan sanda, Major Janar EPA shugaban intelligence na tsaro, Col. Adebisi Onasanya kwamandan birget, Lt-Col Moshood Abiodun Yusuf Guard Battalion na Asokoro Abuja.
Lt-Col Auwalu Baba Inuwa 177 Guard Battalion na keffi Jihar Nasarawa. Lt-Col Mohammed J Abdulkarim 102 Guards Battalion, Suleja na jihar Niger, Lt.- Col. Olumide A. Akingbesote, 176 Guards Battalion, Gwagwalada na Abuja.
Shugaban kasa ya amince da zaben sojojin Fadar shugaban kasa na Villa, Maj.- Isa Farouk Audu Commanding Officer State House Artillery, Capt. Kazeem Olalekan Sunmonu Second-in-Command, State House Artillery.
Maj. Kamaru Koyejo Hamzat, Commanding Officer State House Military Intelligence, Maj. TS Adeola Commanding Officer State House Armament, Lt. A. Aminu Second-in- Command, State House Armament.
Tinubu ya kara da zaben masu bada shawara guda biyu, Hadiza Bala Usman Mai bada shawara kan tsatsaren dokoki. Hannatu Musawa mai bada shawara kan Al’ada da tattalin arzikin nishadi. Da Kuma manyan masu taimaka wa shugaban kasa, Sanata Abdullahi Gumel mai taimako kan Majalisan dattawa.
Olarewaju kunle Ibrahim Mai taimako kan lamarin Majalisan tarayya ta kasa.
Shugaban kasan ya zabi Adeniyi Bashir mai rikon kwaryar kwantrola janar na kwastam.
“A halin yanzu zaben hafsoshin, da shugaban yan sanda da na kwastam zasu cigaba da aiki kamin a tabbatar dasu yanda dokar kasa ta Najeriya ta tsara.” Cewar sa.