Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya zabi kwamishinan goma sha tara da mambobin executive council na jiha. Wanda ake jiran amincewar Majalisan jiha.
Cikin wanda aka zaba sun hada da Hon Ali Haruna Makoda tsohon shugaban Ma’aikatan tsohon gwamna Abdullahi Ganduje, da Hon. Nasiru Sule Garo dan uwan dan takarar mataimakin gwamna a jam’iyyar APC a zaben da ta gabata 2023 Murtala Garo.
Gwamnan ya mika sunayen guda goma sha tara wa Majalisan jiha dan tantancewa.
Shugaban Majalisan jiha Hon. Jibril Ismail Falgore ya bayyana sunayen a zaman ta majalisa ranar talata.
Bayan karanta sunayen, Majalisan ta bukaci wanda aka turo sunayen su da su halarci tantancewa a Majalisan jiha ranar laraba.
Takardar ta bayyana cewa. “Dai dai da karfin da doka gwamnatin Najeriya ta bani, Zan mika takardan sunayen kwamishinan da aka zaba dan tantancewa da amincewa na jihar Kano.
Sunayen da gwamna Abba Kabir Yusuf ya turo sun hada da:
1- Comrade Aminu Abdulsalam
2- Hon. Umar Doguwa
3- Hon. Ali Haruna Makoda
4- Hon. Labaran Abubakar Yusuf
5- Hon. Danjuma Mahmoud
6- Hon. Musa Shanono
7- Abbas Sani Abbas
8- Haj. Aisha Saji
9- Haj. Ladidi Garko
10- Dr. Marwan Ahmad
11- Engr. Muhd Diggol
12- Hon. Adamu Aliyu Kibiya
13- Dr. Yusuf Kofar Mata
14- Hon Hamza Safiyanu
15- Hon. Tajo Usman Zaura
16- Sheikh Tijjani Auwal
17- Hon. Nasiru Sule Garo
18- Hon. Haruna Isa Dederi
19- Hon. Baba Halilu Dantiye