Labaran YauNEWS

Mutuminda Yafi Kowa Search A Google/Internet Ya Musulunta

Mutuminda Yafi Kowa Shahara A Internet Duk Duniya Ya Musulunta

Yau neh daya daga cikin jami’inmu na Labaranyau yaci karo da wani rubutu da wani matashi yayi akan mutuminda yafi kowa shahara a duniya.

Ga abinda Muhammad Abdulrahman Sheka rubuta daga bisani ⇓

Mutumin da yafi kowa shahara a internet ya Musulunta, shine wanda kafin fara yakin Russia da Ukraine yafi kowane dan Adam yawan search a Google amma yanzu Putin Shugaban Russia ya fishi. Dan Kasar America, kuma tsohon dan boxing ne, amma yanzu ya bar boxing. Hakanan Allah Yayi masa tarin dukiya mai yawan gaske.

DOWNLOAD MP3

Tun kafin Musuluntar Andrew Tete ya kasance mutumin da yake masifar kyamatar irin rayuwar dabbanci da turawa suke yi. Hakan yasa watan daya wuce akayi banning dinsa daga kowane social media Facebook, Instagram, Tiktok, Twitter da sauransu. Mutum ne wanda ko lokacin da ba Musulmi ba yana da wasu dabi’u wanda Musulmi kadai suka kebanta dashi.

Bari kuji wasu daga maganganun Mutuminda Yafi Kowa Search A Google Internet Ya Musulunta

1. Musulmi ne kadai suke da wasu dokoki wanda duk rintsi bazasu taba yarda a taka musu su ba.

(Andrew Tete)

DOWNLOAD ZIP

2. A yanzu haka zan iya saka riga wacce a bayanta aka rubutu jesus gay ne kuma ba abinda zai faru koda kuwa ace a cikin garin italy ne (wa’iyazubilahi). Ya kara da cewa amma da zan gwada haka akan Annabin musulmi toh bazan taba koma gida a raye ba ina tafiya akan titi ba za’a samu wani ya datse kaina, kuma ba a cikin Saudi Arabia ba, ko a kasar da aka fi kowacce kasa Addinin kiristanci “Italy” ban isa nayi haka ba.

(Andrew Tete)

3. Har abada bazan taba yadda da idea ta feminist akan cewa mace ta zauna batayi aure ba, tayita neman maza abinda har ta tsufa.

(Andrew Tete)

4. Yanzu ankai matakin da addinin kiritanci ya zama wasa. Mayan maluman kiristoci sun yarda a addinin su zaka iya komai ba matsala. Mafiyawancin masu yin film din batsa kiristoci ne, sune mayan yan luwadin duniya, duk wani mummunan laifi a duniya kiristoci ne suka fi yi, bance musulmi basa yi ba, amma dai ko suna yi suna tsoron yi.

(Andrew Tete)

5. Idan har addini zai yi jure komai, toh wannan ba addini bane. Kafin addini ya cika addini dole sai ya samu wasu dokoki da yake akan su. Musulunci ne kadai yake da wannan suffar.

(Andrew Tete)

6. Ina da tsananin mutuntawa ga musulmi, musamman idan na kalli yadda suke da imani akan addinin su. Mutane suna cewa ai musulunci yayi tsauri da yawa, ni kuma abinda nake fada musu shine. Da yawan dokokin da musulmi suke dasu akawai su a bible, kawai dai ku kiristoci ne bakwa karantawa.

(Andrew Tete)

7. Matan musulmi da kuke ganin su a gida, sunfi wadannan wawayen yan matan namu da kuke gani suna rawa a club rayuwar farin ciki.

(Andrew Tete)

8. Daga cikin kasashen da suka fi kowane kasashe a duniya kasashen musulmi ne. Zaka iya zuwa kasar Qatar na kwanta tare da miliyoyin kudi akan titi, kuma ba abinda zai same ka, kai karshe ma idan kaje dubai zakaga suna faka motocin su ne tare da mukullin a ciki. Duk wasu matsaloli da muke dasu anan America babu su a kasashen musulmi, kuma addinin su ne yayi sanadin hakan.

(Andrew Tete)

9. Ni kaina shekaru bakwai da suka wuce ina kan akidar mulhidanci “Atheist” addinin bautar shaidan, daga baya kuma bayan na fara bibiyar musulmi sai na gano cewa ai akan shirme nake, tunda babu yadda za’a yi ka yarda da shaidan kuma baka yarda akwai Allah ba.

(Andrew Tete)

10. Duk wata matsala da kuke gani ana fama da ita a yanzu haka a duniya, musulunci ya riga ya kawo mafita ga matsalar.

(Andrew Tete)

ALLAH YASA MUSULUNTAR SA TA AMFANI MUSULUNCI DA MUSULMI.

Author: Muhammad Abdulrahman Sheka

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button