Labaran Yau

BAKIN HALI!! An Kama Yar Aikin Gida Tanasa Guba A Abincin Mai Gida (VIDEO)

Wani faifan bidiyo nata karade yanar gizo yau safiyar Laraba wanda ke nuna yadda aka kama wata matashiya mai yin abinci da wanke wanke da ake zargin ta da sanya guba a miyan Iyalan gida.

Rahotanni sun bayyana cewa, yarinyar ta kara guban bera a cikin tukunyar miya wanda ke ajiye a cikin kitchen.

An tanada miyan ne domin abincin iyalan gida baki daya, tayi hakanne bayan an kwace wayarta a matsayin hukuncin ladabtarwa saboda wani laifin da ta aikata a baya.

Daya daga cikin wanda suka kamata ke tambayanta ko zata iyi cin miyar da ake zargin ta sa guba a ciki? Sai ta amsa da “A’a”.

Allah ya kyauta, amma yakamata mutane su ringa bincika yaran da suke dauka a matsayin masu aiki saboda wasunsu ba tsakani da Allah suke aikin ba.

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button