Labaran Yau

Ma’aikatan Shari’a Ta Kasa Sun Bayyana Tafiya Yajin Aiki Saboda Tashin Farashin Kudin..

Ma’aikatan Shari’a ta kasa sun bayyana tafiya yajin aiki saboda tashin farashin kudin man fetur

Ma’aikatan Kotu na kasa (JUSUN) sun bayyana cewa zasu shiga yajin aiki saboda tashin Farashin Mai da ya auku saboda cire tallafi da gwamnati tayi. Farashin man fetur ya ninka sau uku bayan shugaban kasa Tinubu ya bayyana cewa tallafin man ya kare.

Hukumar kwadigo ta kasa ta bayyana tafiya yajin aiki wanda za’a fara ran laraba.

A bayanin, Sakatare Janar na Ma’aikatan shari’a M.J Akwashiki, ya bada umurnin duk wani kungiya dake karkashin su da su bar aiki ranan Laraba.

“Hakan yazo ne bayan hukuncin da Hukumar kwadigo ta yanke bayan zaman da sukayi na biyu ran 2 ga watan Yuni, kan tashin farashin man fetur wanda gwamnatin tarayya tayi karkashin NNPCL” a cewar sa.

“Duka mataimakan shugaban zasuyi gudanar da yankunan su da kuma kananan ciyamomin su dasu tabbatar mambobin su sun bi dokar.”

Daily trust ta rawaito

Join Our:  WhatsApp Group  |  Telegram

Watch African Stories

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button