Kwararren dan wasan me suna Mustafa Othman dan shekara 40 ya samu nasarar lashe babbar gasar chess na North East Zonal Championship a 2024.
Wasan an fafa tane a makon daya gabata na wannan watar Yuli, wanda aka fafata tsakanni kwararru yan wasan chess daga jiha daban daban na kwana uku.
Kowanni dan wasa ya wakilci jiharsane a babbar gasan ta tsakannin jihohi daga shashin arewa maso gabas wanda ya kunshi garurruka kamar haka: Jihar Taraba, Gombe, Adamawa, Borno, Bauchi, da Yobe.
Mustafa Othman dan jihar Bauchi kuma me wakiltan jihan a babbar gasan, ya lashe gasanne cikin kwanciyan hankali, dubi da irin tarihin sa a matsayin dan wasan ch-ess din a gaba daya duniya.
Me nasarar gasar, yanada kyakkyawar matsayin mataki a manhaja da kungiyar che-ss na gaba daya duniya, ya kasance jajir cecce wurin lissafi da dabar barun wasan chess din.
Bugu da kari kishin jiharne yasa ya wakilci jihar kuma ya tabbatar da kawo nasara kamar yanda ya fada kafin tafiyarsa.
Jawabinsa bayan samun nasara na lashe babbar gasan yayi nuni dacewa a shirye yake domin wakiltan jiharsa a kowata irin matakine na wasan chess har ma ya kara da darasi da kari fahimtar dabaru daya samu a wannan gasa.
Mustafa Othman yace kamar haka: “Naji dadin kawo wa jiha ta nasara kuma nayi farin cikin dawainiyarta akan wasan, asshirye nake don ci gaba da wakiltan ta a kowani irin rukuni”.
Sannan nakara samun basira wurin gane rauni na a kan tattalin lokaci wanda abune me matukar amfani a wasar chess, kuma da ikon Allah zan kara dagewa wurin ganin na shakan wannan cikin kwarewa”
A shafin mata na gasan ch-ess din yankin arewa gaba daya, mace mai suna Rejoice Ishaya ce ta samu nasarar lashe gasan. Wanda ta nuna matukan murnan ta wurin samun nasarar.
Bayan haka ta nuna godiyan ta a kan kokari da gomnati tayi wurin saukaka samun daman halartar gasan don cinma burin yan wasa daga kowan mataki na rayuwa.
KOYI YANDA AKE BUGA WASAN CHESS CIKIN SAUKI